MDD ta koka kan karuwar cin zarafin mata a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo

MDD ta koka kan karuwar cin zarafin mata a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo

An yi kiyasin cewa mutum miliyan takwas ne ke neman agajin gaggawa a larduna uku da yaki ya fi shafa a kasar.
MDD ta ce ana matukar bukatar jin kai a wasu larduna na Jamhuriyyar Kongo. Hoto/AP

Matsalolin jinkai a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo wadda yaki ya daidaita na karuwa matuka a watanni 18 da suka gabata, inda akalla mutum miliyan takwas suke bukatar agajin gaggawa, kamar yadda wata babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Edem Wosornu, daraktar jinkai ta MDD wadda ba ta jima da dawowa daga Kongo ba tare da wasu daraktoci na bayar da agajin gaggawa na MDD da sauran kungiyoyi, ta bayyana cewa irin abubuwan da suka ji kuma suka gani “lamari ne mai ban mamaki kuma mai ban tsoro da damuwa”.

Ta ce yara mata na matukar fuskantar barazanar cin zarafi ta hanyar lalata musamman a larduna uku na kasar.

Wosornu ta bayyana cewa yadda lamarin yake a Arewaci da Kudancin lardunan Kivu da kuma lardin Ituri, “a gaskiya shi ne lamari mafi muni da muka taba gani,” kuma hakan na faruwa ne a kasar da ke da sama da mutum miliyan 26 da suke cikin yunwa da kuma bukatar abinci.

Wosornu ta shaida wa taron manema labarai cewa ta’addanci wanda ya danganci jini “na kara yaduwa fiye da tsammani” inda sama da mutum 35,000 wadanda suka tsira suke neman magani bayan an far musu a cikin watanni shida na 2023 a larduna uku.

Duk da cewa adadi kadan ne na wadanda aka ci zarafinsu sakamakon jinsinsu ne ke kai kara karuwa, ta bayyana cewa, “akwai yiwuwar adadin ya karu”.

Rikici yana ta karuwa tsawon shekaru a yankunan Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo mai dumbin arzikin ma’adinai inda Wosornu ta ce sama da kungiyoyi na masu rike da makamai 130 suke rikici musamman domin samun iko da filaye da wuraren hakar ma’adinai, duk da cewa wasu kungiyoyin na son kare al’ummominsu.

Rikici ya yi matukar karuwa a karshen 2021 a lokacin da ‘yan tawayen M23, wadda kungiya ce ta ‘yan tawaye wadda aka alakanta da Rwanda mai makwaftaka wadda kungiyar ta shafe shekaru ba ta kai hare-hare amma ta farfado inda take kwace iko da yankuna.

M23 ta kara karfi a 2012 a lokacin da mayakanta suka kwace iko da Goma wanda birni ne da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo wanda ke kan iyaka da Rwanda.

Ba da jimawa ba, wasu hare-hare da kungiyar Allied Democratic Forces ta ADF take kaiwa wadda ake ganin tana da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ya kara ta’azzara rikicin da ake yi yi na cikin gida.

Gabriella Waaijman, ita ce daraktar jin kai ta duniya a kungiyar Save the Children da ke London wadda ita ma tana daga cikin wadanda suka ce Kongo, ta bayyana cewa kasar ke da adadi mafi yawa na wadanda aka ci zarafinsu.

Haka kuma ta bayyana cewa kasar ita ke da adadi mafi yawa a duniya na wadanda suka rasa muhallansu – haka kuma adadin wadanda suka rasa muhallan nasu ya karu da miliyan guda a bana.

Sakamakon karin wahalhalu da kuma karancin kudi ya bar ma’aikatan agaji cikin wani mawuyacin hali a kullum inda suke tunani a koda yaushe kan ko dai su bayar da fifiko kan ruwa ko matsuguni ko kiwon lafiya ga sabbin wadanda suka rasa muhallansu.

Haka kuma wata karin bukatar ita ce dubban yara ba su iya zuwa makaranta, in ji ta. Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a bayar da dala biliyan 2.3 a matsayin kudin tallafin jin kai ga Kongo a bana sai dai kasar ta samu dala miliyan 764 ne kacal, Wosornu ta ce kudaden sun iya taimakon mutum miliyan 1.4 ne kacal, “inda adadi ne kadan daga cikin mabukata.”

Rukunin na daraktoci ya hadu da ministan ayyukan jin-kai na Kongo da kuma gwamnonin soji na Ituri da Arewacin Kivu inda suka bukaci a kara matsa kaimi wurin kare farar hula, da kuma muhimmancin hukumomi wurin dakile cin zarafin jinsi da kuma matukar amfanin dawo da zaman lafiya wanda shi ne abin da duk wanda suka hadu da shi yake nema, in ji ta.

Waaijiman ta bayyana cewa ana matukar bukatar kudi domin samun karin taimako don ceto rayukan al’umma amma abin da mutane ke bukata a halin yanzu shi ne zaman lafiya “da kuma gwamnatinsu ta mayar da hankali wurin ganin sun koma gidajensu lafiya ko kuma ta ba su filaye wadanda za su soma sabuwar rayuwa.”

Ma’adinai masu dumbin yawa da ke a Kongo sun jawo yaki, da raba mutane da muhallansu da yunwa, kamar yadda ta bayyana.

AP