Deby ya shaida wa manema labarai a Yankin Tafkin Chadi cewa, "mun kai hare-hare ta sama da dama a kan wuraren da abokan gaba suka yi sanadin mutuwar mutane da dama."

Sojojin kasar Chadi sun yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram da dama da kuma jikkata wasu a hare-haren da suka kai wa kungiyar ta sama, in ji shugaban kasar Mahamat Idriss Deby Itno a ranar Alhamis.

Deby ya shaida wa manema labarai a Yankin Tafkin Chadi cewa, "mun kai hare-hare ta sama da dama a kan wuraren da abokan gaba suka yi sanadin mutuwar mutane da dama."

Deby, wanda aka yi hira da shi yana sanye da kakin soji, ya ce shi da kansa ya kaddamar da farmakin tunkarar mayakan Boko Haram, wadanda suka kai wa sojojin Chadi hari a watan da ya gabata a yankin yammacin kasar, kusa da kan iyaka da Nijeriya.

Gwamnatin Chadi ta sha alwashin kawar da Boko Haram a lokacin da ta kaddamar da farmakin a karshen watan Oktoba bayan da mayakan kungiyar suka kashe mata sojoji kusan 40 tare da jikkata wasu da dama a wani samame da suka kai a wani barikin soji.

Wannan farmakin “ba wai don tabbatar da zaman lafiyar al’ummarmu kawai aka yi shi ba” har ma da “farauta da tumbuke da kuma kawar da karfin kungiyar Boko Haram da sauran ‘yan ta’addan da suke da alaka da su a wajen yin barna,” in ji Firaministan wucin gadi na kasar Abderahim Bireme Hamid ga manema labarai a makon da ya gabata.

A cikin faffadan ruwa da fadama, tsibiran yankin Tafkin Chadi marasa adadi sun zama maboya ga kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Boko Haram da mayakan kungiyar IS a yammacin Afirka (ISWAP), wadanda ke kai hare-hare akai-akai kan sojojin kasar da fararen hula. .

Kasar Chadi da makwabtanta Nijeriya da Nijar da Kamaru sun kafa rundunar kasa da kasa mai dauke da sojoji kusan 8,500 a yankin a shekarar 2015 domin tunkarar 'yan ta'adda.

Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a Nijeriya a shekara ta 2009, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000, kuma kungiyar ta yadu zuwa kasashe makwabta.

A watan Maris din shekarar 2020, sojojin kasar Chadi sun yi asara mafi girma ta kwana guda a yankin, lokacin da sojoji kusan 100 suka mutu a wani samame da suka kai a gabar Tafkin Bohoma.

AFP