Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta ce ta yi nasarar kashe '‘yan ta’adda' masu satar mutane don karbar kudin fansa da dama a wani harin sama da ta kai a Jihar Kaduna.
A sanarwar da rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun Daraktan Watsa Labaranta Air Vice Marshal Edward Gabkwet a ranar Litinin, rundunar ta ce ta kai harin ne a ƙoƙarin da take ci gaba da yi na magance ta’addanci da satar mutane a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar kasar.
“An kai harin ne bayan samun wani rahoton sirri a kan wani gungun ƴan ta’addan a kan titin Kwiga-Kampamin Doka da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna,” in ji sanarwar.
Ta kuma ce an gano cewa gungun mutanen su ne waɗanda suka yi wa sojojin rundunar 'Kwanan Mutuwa' kwanton ɓauna ranar Asabar 27 ga watan Janairu, tare da kai hare-hare da dama da sace mutane a Birnin Gwari.
Da take bayanin yadda ta yi nasara a wannan hari da ta kai, rundunar sojin ta ce “bayan da dakarunmu suka isa yankin, sai aka yi wani bincike da ya nuna yadda tawagar ƴan ta’addan suke tafiya a kan babura 15, inda kowane babur ke dauke da aƙalla mutum biyu ɗauke da makamai.
“An kashe ƴan ta’adda da yawa a sakamakon harin saman da aka kai musu,” sanarwar ta fada.
Sai dai babban hafsan rundunar sojin saman Air Marshal Hasan Abubakar wanda ya yabi dakarun da suka yi aikin, ya yi gargadin cewa dole a ci gaba da kokarin da ake yi.
“A yayin da muke farin cikin wannan nasara, dole na yabi ƙwarewar tawagar nan da suka yi jimirin bin diddigin miyagun har sai da aka samu damar da ta fi dacewa kafin kai harin. Dole mu ci gaba da jajircewa da yin abin da ya kamata,” in ji shi.