Shugabanni daga fadin duniya na ta nuna alhininsu kan girgizar kasar da ta faru a Tsaunukan Atlas na Maroko a ranar Juma’a da dare inda daruruwan mutane suka rasu tare da lalata gine-gine da dama.
Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta nuna alihininta kan wannan girgizar kasar wadda ta jawo dumbin asara.
Kasar Turkiyya ta ce tana tare da Maroko inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce “Ina mika fatan alherina ga duka jama’ar da bala’in girgizar kasa ya shafa a ‘yar uwarmu Maroko”.
Shugaba Erdogan ya roki Allah Ya yi wa wadanda suka rasu sakamakon girgizar kasar rahama sai kuma wadanda suka samu raunuka ya yi musu addu’ar samun sauki.
Sama da mutum 600 aka tabbatar sun rasu zuwa yanzu sakamakon wannan girgizar kasar a daidai lokacin da ake ci gaba da aikin ceto. An ji karar girgizar kasar a kasashen da ke makwaftaka.
“Muna addu’a ga duka wadanda suka samu raunuka su samu sauki cikin gaggawa.
Gaba daya al’ummar duniya na tare da Maroko a wannan lokacin mai tsanani kuma a shirye muke da mu ba su duk wata gudunmawa,” kamar yadda Firaiminstan India Narendra Modi ya bayyana a taron G20 wadda kasarsa ke karbar bakunci.
Shi ma Firaiministan Sifaniya Pedro Sanchez ya bayyana wannan girgizar kasar a matsayin mummuna.
“Duka goyon bayana na tare da al’ummar Maroko a lokacin wannan mummunar girgizar kasar...Sifaniya na tare da wadanda wannan girgizar kasar ta shafa da iyalansu,” in ji Sanchez.
Ita ma Firaiminisar Faransa Catherine Colonna ba a bar ta a baya ba inda ta ce “Goyon bayanmu ga kasar Maroko da abokanmu ‘yan Maroko bayan wannan mummunar girgizar kasar ta dare.
“Muna tausaya wa wadanda abin ya shafa da iyalansu da kuma jinjina ga masu aikin ceto wadanda suke ta jajircewa wurin taimakom wadanda suka samu rauni,” in ji Ministar Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna.