Wannan ziyara dai na cikin ziyarar Ramadan da babban sakataren ke kai wa kasashen Musulmi kowace shekara / Photo: AA

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya isa kasar Somaliya a wani bangare na ziyarar Ramadan da yake yi duk shekara, wadda ya fara tun yana shugabantar hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD.

Antonio Guterres ya isa Mogadishu, babban birnin Somalia ranar Talata, don gajeriyar ziyara a kasar da ke farfadowa daga shekarun da ta shafe tana fama da yake-yake da matsalolin sauyin yanayi.

Hotuna a shafukan sadarwa sun nuna lokacin da Ministan Harkokin Waje na Somaliya, Abshir Omar Huruse yake maraba da Antonio Guterres a filin jirgin sama da ke babban birnin kasar.

Ana sa ran Antonio Guterres zai zanta da shugabannin kasar kan batutuwa masu alaka da rashin tsaro, da illolin sauyin yanayi, da ayyukan jin-kai a kasar.

Wannan ziyara dai na cikin ziyarar Ramadan da babban sakataren ke kai wa kasashen Musulmi kowace shekara.

A farkon makon nan, Antonio Guterres ya ce a wani sakon Twitter, “A ganina, al’adata ta ziyarar Ramadan wata dama ce ta tunawa da muhimmancin assasa zaman lafiya a duniya. Dama ce ta samun ilhama.”

Haka kuma Mista Guterres ya jaddada kiran hadin kai tsakanin mabambantan al’ummomin addinai, inda yake cewa, “Mu zo mu hadu don kishin juna, ba tare da duba bambancin addininmu ba.”

Kasar Somaliya ta saka takunkumin hana zirga-zirga a garin Mogadishu dalilin wannan ziyarar. Hakan ya janyo an rufe yawancin tituna da hanyoyin sufuri.

Antonio Guterres yana ziyartar kasar ne wadda ke cikin kangin fari da ke barazanar janyo karancin abinci, baya ga kasancewar gwamnatin kasar na yakar ta’addanci da bore daga kungiyar Al Shabaab.

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar neman tara dala biliyan 2.6 don ayyukan jin-kai ga yankin kusurwar Afirka, duk da dai zuwa yanzu kashi 13 na kudin kawai aka iya tarawa.

Shekaru biyar a jere na rashin ruwan sama a yankunan Somaliya da Kenya da Habasha, sun haifar da mafi munin fari a cikin shekaru 40 a yankin.

Hakan ya haddasa mutuwar dabbobi da tsirrai, da kuma tagayyarar mutum miliyan 1.7 daga gidajensu zuwa neman abinci da ruwa.

Yayin da aka kusa cimma matakin rashin abinci a Somaliya, Majalisa Dinkin Duniya ta ce kusan rabin al’ummar kasar za su bukaci taimakon jin-kai a wannan shekara, sannan mutum miliyan 8.3 farin ya shafa.

Antonio Guterres ya fara al’adarsa ta ziyarar Ramadan lokacin yana Babban Kwamishinan ‘yan gudun hijira, inda ya jagoranci hukumar ta UNHCR tsawon shekara 10, kafin daga bisani ya karbi ragamar MDD a shekarar 2017.

A shekarar da ta gabata, ya ziyarci Nijeriya, da Nijar da Senegal, inda ya tabo batutuwan rashin tsaro, da sauyin yanayi, da tasirin yakin Rasha da Yukren kan samar da abinci a duniya.

Ya kuma yi kira kan hadin kai tsakanin al’ummomi masu bin addinai daban-daban.

TRT Afrika