Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya yi matukar damuwa game da "mawuyacin halin" da shugaban Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa ke ciki sakamakon tsarewar da sojoji suke yi musu.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar ranar Laraba.
Sanarwar na zuwa ne bayan Mohamed Bazoum ya yi korafin cewa sojojin da suka yi masa juyin mulki sun tsare shi a wani wuri sannan suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya.
"Sakatare Janar yana jaddada damuwarsa game da koshin lafiya da tsaron shugaban kasa da iyalansa kuma yana kara kira da a sake shi nan take ba tare da wasu sharudda ba kuma a mayar da shi kujerarsa ta shugaban kasa," a cewar sanarwar da kakakin Guterres ya fitar.
Ranar Laraba wani makusancin Mohamed Bazoum ya ambato shi yana cewa abinsa da na iyalansa ya kusa karewa kuma an yi garkuwa da su a wani wuri cikin mawuyacin hali.
Ya kara da cewa gidan da suke ciki babu hasken lantarki sannan sannan ba sa iya yin komai tun da aka tsare su bayan sojoji sun yi masa juyin mulki ranar 26 ga watan Yuli.
Jam'iyyar PNDS Tarayya ta Shugaba Bazoum ta tabbatar da mayuacin halin da yake ciki.
Taron ECOWAS
A yau ne kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta gudanar da taro kan matakin da za ta dauka bayan wa'adin da ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya kare.
ECOWAS ta bai wa sojojin wa'adin mako guda ne su mayar da Bazoum kan mulki ko su fuskanci yiwuwar amfani da karfin soji.
Sai dai sojojin sun yi fatali da umarnin sannan suka ce za su yi martani mai karfi kuma "cikin gaggawa kan duk wani kutse daga kasashen waje".
Sanarwar kungiyar ta ce "shugabannin ECOWAS za su yi nazari da tattaunawa game da halin siyasa da abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan a Nijar."
Taron nasu na zuwa ne kwana guda bayan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya gana da jagoran masu juyin mulki Janar Abdourahamane Tchiani a Yamai don samun hanyar kawo karshen wannan kiki-kaka.