Shugaban Kenya William Ruto ya sanya sunayen manyan 'yan adawa da kuma wasu ministocin da ya sallama a baya, a jerin sabbin ministocin da ya faɗaɗa, bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da ta yi sanadin fiye da mutum 50.
Shugaban Ƙasar ya ambaci sunan shugaban marasa rinjaye Opiyo Wandayi a matsayin ministan makamashi da ɗan majalisa John Mbadi a matsayin minsitan kuɗi, waɗanda dukkansu 'yan jam'iyyar adawa ta Raila Odinga ce.
A ranar Laraba ne Ruto ya bayyana sunayen ministoci 10 a jeri na biyu da ya fitar da suka haɗa da ministoci huɗu da atoni janar ɗin da ya sallama daga aiki mako biyu da suka wuce.
A makon da ya wuce ne ya bayyana jerin farko na ministocin.
Mambobin Majalisar Dokokin Ƙasar sun amince da sunayen ministocin da Shugaban Ƙasar ya miƙa musu.
Ga dai cikakken jerin sunayen ministocin Kenyan da Shugaban Ƙasa ya zaɓa: