Ken Ofori-Atta / Photo: Reuters

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya cire ministan kudin kasar Ken Ofori-Atta daga mukaminsa, a daidai lokacin da kasar ke kokarin farfado da tattalin arzikinta.

Tun a shekarar 2017 Mista Oforri- Atta yake riƙe da muƙamin ministan kuɗi na Ghana, inda ya yi ta fuskantar suka kan taɓarɓarewar da tattalin arzikin ƙasar ke yi.

A shekarar 2022 matsalar ta daɗa ƙamari inda hauhawar farashin kayayyaki ta zarce kashi 50 cikin 100 sannan gwamnati ta gaza biyan lamuni.

Daga baya ta sake fasalin biyan bashinta da masu ba da lamuni don samun cancantar tallafin IMF.

A ranar Laraba ne aka naɗa Mohammed Amin Adam wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin ministan makamashi da kuma ƙaramin minista a ma’aikatar kuɗi a matsayin wanda ya maye gurbin Mista Ofori-Atta.

Ana sa ran Mista Adam zai sa ido kan shirin farfaɗo da tattalin arzikin na dala biliyan 3 daga IMF da ake ci gaba da yi da kuma batun sake fasalin basussukan masu ba da lamunin kasuwanci a ƙasar.

Shugaba Akufo-Addo ya maye gurbin wasu ministocinsa 12 a shirin sauya majalisar ministocin da aka yi ranar Laraba, gabanin zaɓen shugaban ƙasar Ghana da za a yi a watan Disamba shekarar 2024.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince