Shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya yi kira ga kungiyar Commonwealth da ECOWAS da su hada kai wajen tabbatar da an saki hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum cikin gaggawa kuma ba tare da wani sharadi ba.
A ranar 26 ga watan Yulin wannan shekara ne sojojin Nijar suka hambarar da Bazoum mai shekaru 63 daga kan mulki kuma har yanzu yana tsare.
Shugabannin juyin mulkin sun bayyana rashin tsaro da kasar ke fama da shi a matsayin hujjar kifar da gwamnatin dimokuradiyya - matakin da ya sha suka sosai daga kasashen duniya .
A jawabinsa yayin bude taron 'yan majalisar dokokin kasashen Commonwealth karo na 66, a birnin Accra, shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya yi Allah wadai da ci gaba da tsare tsohon shugaban Nijar ba tare da wata hujjar yin hakan ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar GNA ya rawaito.
Ya ce irin sauye-sauyen da ake samu wadanda suka saba wa tsarin mulkin dimokaradiyya a yankin Afirka, musamman ta hanyar sa hannun sojoji a harkokin mulki, kamata ya yi kowa ya hada kai wajen ganin an yi wasti tare da dakatar da hakan.
"Dole ne mu ci gaba da tsayin daka wajen yin Allah wadai da ayyukan da ke kutse ga tsarin dImokUradiyya, " in ji shi.
Shugaban ya ce bin tsarin mulkin dimokuradiyya da kundin tsarin mulki na da matukar muhimmanci wajen samar da kwanciyar hankali da wadata a Afirka.
Wadannan al’amura da kuma karuwar hare-haren ayyukan ta’addanci da sauran munanan abubuwa sun taimaka wajen tabarbarewar yanayin tsaro a yankin na Afirka, a cewar Nana Akufo-Ado.