Shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi ya amince da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa, a wani mataki da ake kallo a matsayin gagarumin koma-baya ga jam'iyyarsa ta Botswana Democratic Party, wadda ke mulkin ƙasar tun 1966.
"Zan miƙa mulki cikin mutunci tare da tabbatar da ganin sabuwar gwamnati ta hau kan mulki ba tare da wata matsala ba," in ji shugaban ƙasar.
Jam'iyya mai mulki a Botswana, BDP, ta rasa rinjayenta a majalisar dokokin ƙasar a zaɓen da aka gudanar a wannan makon, kamar yadda jaridar Mmegi mai zaman kanta ta ruwaito ranar Juma'a, inda ta ambato sakamakon zaɓe daga fiye da rabin mazaɓun ƙasar.
Masu sharhi sun yi hasashen cewa fafatawa za ta yi zafi duk da cewa suna ganin rarrabuwar kan 'yan adawa za ta bai wa jam'iyyar Shugaba Mokgweetsi Masisi damar rinjaye.
Jam'iyyar ta BDP ta mulki ƙasar ta kudancin Afirka mai mutane miliyan 2.3 tun lokacin da ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1966.
Zaman lafiya
Jaridar Mmegi ta ce sakamakon zaɓen daga mazaɓu 36 cikin mazaɓu 61 na ƙasar ya nuna cewa jam'iyyun adawa sun lashe fiye da rabin kujeru na majalisar dokokin ƙasar.
Gidan rediyo mallakar kasar ma irin wannnan sakamakon ne ta fitar. Ta ce kawo yanzu jam'iyyar BDP mai mulki ta yi nasara ne a mazaba daya tilo cikin mazabu 36. Wata gamayyar jam'iyyun adawa ta UDC ta yi nasara a mazabu 23.
Ko wace jam'iyya tana bukatar lashe kujeru 31 kafin ta kasance mai rinjaye a wannan zaben.
Botswana ta sami zaman lafiya da kuma wanzuwar arziki domin arzikinta na lu'ulu'u da kuma karancin jama'arta wadda ke samun kiwon lafiya da ilimi kyauta.
Koma-baya a kasuwar lu'ulu'u
Ita ce kasar da ta fi samar da dutsen lu'ulu'u mai daraja.
Amma koma-baya a kasuwar lu'ulu'u din ya rage kudin shigar kasar cikin 'yan shekarun nan, kuma kasar na fama da kalubale wajen samar da sabbin hanyoyin kudaden shiga ga tattalin arzkinta