Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka Joe Biden a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a watan gobe, a cewar mai magana da yawunsa.
Za a gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ne daga ranar 18 zuwa 26 ga watan Satumba a birnin New York.
Wata sanarwa da Ajuri Ngelale, kakakin Shugaba Tinubu ya fitar ranar Asabar ta ce shugaban kasar ya amince da gayyatar da shugaban Amurka ya yi masa ta hannun wakilin shugaban kasar da kuma mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka a kan harkokin Afirka Molly Phee.
Mai yiwuwa shugabannin biyu su tattauna a kan rikicin siyasar da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, inda Shugaba Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS, yake aiki da sauran shugabannin Yammacin Afirka domin shawo kan matsalar.
Tinubu, wanda ya soma aiwatar da manyan sauye-sauye kan tattalin arzikin Nijeriya, ya yi kira ga Amurka ta zuba karin jari a kasar sannan ta karfafa dangantaka ta fuskar kare mulkin dimokuradiyya a Yammacin Afirka, a yayin da juyin mulki ke neman zama abin da ake yayi a yankin.