Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kudurin kasafin kudin 2024 na naira tiriliyan 28.77.
Ya sanya hannu kan kasafin kudin ne ranar Litinin a fadarsa da ke Abuja, a gaban shugabannin Majalisun Dokokin Tarayya da Ministoci da manyan jami'an gwamnatinsa.
Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mr Ajuri Ngelale ya fitar ranar Litinin da maraice ta ambato Shugaba Tinubu yana cewa kasafin kudin zai mayar da hankali kan harkokin "tsaro da tsaron cikin gida da samar da ayyukan yi da daidaita harkokin tattalin arziki da bunkasa yanayin zuba jari da rage talauci da samar da walwala."
Labari mai alaka: Majalisun Dokokin Nijeriya sun amince da Naira Tiriliyan 28.77 a matsayin kasafin kudin 2024
Shugaba Tinubu ya jaddada aniyarsa ta bunkasa fannin zuba jari da samar da yanayin da kowanne dan kasar zai yi biyayya ga doka ba tare da nuna son kai ba, yana mai cewa hakan zai fara ne da yin garambawul ga fannin shari'a, inda aka ware kudaden aiwatar da wannan shiri a cikin kasafin kudin.
"Samar da kudi ga fannin shari'a babban mataki ne a yunkurinmu na samun al'umma mai adalci da bin doka. An kara yawan kasafin kudin fannin shari'a daga naira biliyan 165 zuwa naira biliyan 342," in ji shugaban Nijeriya.
Ya kara da cewa za a kashe naira tiriliyan 10 wajen gudanar da manyan ayyuka da naira tiriliyan 8.8 a ayyukan yau da kullum da naira tiriliyan 8.2 domin biyan bashi.