Kalamin da shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya ya yi cewa ba da yawunsu shugabannin majalisun dokokin kasar suka nada manyan jagororin majalisun ba ya tayar da kura a kasar inda wasu ke ganin an soma samun takun-saka tsakanin bangarorin biyu.
Ranar Talatar da ta wuce ne shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas suka sanar da sunayen jagororin majalisun wadanda suka hada da shugabannin masu rinjaye.
Sai dai shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Adamu ya yi watsi da wannan mataki wanda ya ce kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar (NWC) bai san da shi ba.
Hakan ne ya sa aka soma ce-ce-ku-ce a fagen siyasar kasar ganin cewa a al’adance ana yin irin wadannan nade-nade ko zabuka ne bayan an yi tattauna tsakanin bangaren majalisun da na zartarwa, wato bangaren shugaban kasa da kuma jam’iyya mai mulki.
Jagororin majalisu
Baya ga shugabannin majalisun tarayya biyu – shugaban majalisar dattawa da na wakilai – ana zabar shugabannin masu rinjaye da mataimakinsa da mai tsawatarwa da shugaban marasa rinjaye da mataimakinsa da sauransu.
A sanarwar da shugabannin majalisun dokokin suka bayar a zauren majalisar, sun ce an zabi Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa yayin da aka nada Julius Ihonvbere matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta Nijeriya.
Tsohon gwamnan Ebonyi David Umahi ya zama Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar dattawa.
An zabi Sanata Mohammed Ali Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa na masu rinjaye da kuma Lola Ashiru a matsayin mataimakinsa.
Sannan kuma Simon Mwadkon shi ne Shugaban Marasa Rinjaye da kuma Oyewumi Olalere a matsayin mataimakinsa.
Majalisar ta kuma sanar da Sanata Darlington Nwokocha a matsayin mai tsawatarwa na marasa rinjaye da kuma Sanata Rufai Hanga wanda ya zama mataimakinsa.
Ita ma Majalisar Wakilai ta zabi Julius Ihonvbere a matsayin Shugaban Masu Rinjaye yayin da Abdullahi Ibrahim Halims ya zama mataimakinsa.
Usman Bello Kumo ya zama Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye, sannan Adewumi Onanuga shi ne Mataimakinsa, inda kuma Kingsley Chinda ya zama Shugaban Marasa Rinjaye.
Ali Isa shi ne ya sabon Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye sai Aliyu Sani Madaki Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye.
Jita-jita
Shugaban jam'iyyar APC Abdullahi ya ce labarin nadin sabbin shugabannin majalisar "jita-jita ne" saboda kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar bai amince da shi ba.
Ya ce kwamitin bai aika sunayen sabbin jagororin ga Akpabio ko Abbas ba.
“Ina jin wannan ne a matsayin jita-jita daga kafafen yada labarai na intanet cewa akwai wasu nade-nade da aka yi a majalisar dattawa da ta wakilai," in ji Abdullahi Adamu.
"Kawo yanzu hedkwatar jam'iyyarmu da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na kasa ba su fitar da sanarwa ba dangane da nadin sabbin shugabannin.
"Sai bayan mun warware da su kuma mun yi rubutu a tsakaninmu, wanda haka da ma al'adar take, kuma ba za mu daina wannan al'adar ba. Saboda haka duk wata sanarwa da aka fitar ba daga jam'iyyar ta fito ba," in ji shugaban APC.
Kokawar neman iko
Masana harkokin siyasa a Nijeriya na ganin wannan turka-turka ce ta neman iko kuma ba wani sabon abu ba ne a siyasar kasar.
Dokta Abubakar Kari, masanin siyasa ne kuma malami a Jami'ar Abuja, ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa wannan lamari "gwagwarmaya ce ta neman iko tsakanin bangarorin jam'iyyar APC daban-daban".
"APC hadaka ce ta jam'iyyu da kungiyoyi kuma har yanzu wannan lamari haka yake. Ita uwar jam'iyya tana ganin hurumimta ne kuma ba a tuntube ba. Tana ganin ya kamata a ce an tuntube ta idan za a nada wadannan jagororin majalisa, amma ba a yi hakan ba," in ji Dokta Kari.
Masanin ya ci gaba da cewa "a bisa tsarin doka majalisa ce za ta zabi shugabanni da jagororinta, amma a al'adance duk inda ake yin tsarin siyasar majalisa, jam'iyya tana da fada aji a game da su waye za su jagoranci majalisa.
A al'adance amma ba shari'ar ce ba. A shari'ance dai majalisa ce take da wannan iko kuma ta yi."
A karshe ya ce "sannu a hankali wannan takaddama za ta wuce. Haka siyasar Nijeriya ta gada. A duk lokacin da aka yi gwagwarmaya wadanda aka kayar za su yi ta guna-guni wadansunsu ma za su yi barazanar zuwa kotu. Amma daga baya ina ganin za su hakura musamman ma ganin fadar shugaban kasa ta goyi bayan wannan abu."