Bayanai sun nuna cewa kafin wannan lokaci yawancin 'yan majalisar suna goyon bayan Betara ya zama shugaban majalisar wakilan Nijeriya. Hoto/ Twitter @OfficialSKSM

Fitattun 'yan majalisar wakilan Nijeriya guda biyu da ke gaba-gaba wajen neman shugabancin majalisar, Muktar Betara Aliyu da Yusuf Gagdi, sun janye takararsu kuma sun goyi bayan Tajudeen Abbas.

Sun nuna goyon baya ga dan majalisar ne bayan sun gana da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ranar Lahadi da daddare.

Honorabul Gagdi daga jihar Filato ya dade yana nuna tirjiya don ganin an bai wa arewa ta tsakiyar Nijeriya damar fitar da shugaban majalisar wakilan kasar ta goma.

Kazalika bayanai sun ce akasarin 'yan majalisar dokokin suna goyon bayan Honorabul Betara kafin wannan lokaci.

Tun makonnin baya jam'iyyar APC mai mulkin kasar da ma Shugaba Bola Tinubu suka nuna goyon bayansu ga Honorabul Tajuddeen Abbas daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar don zama shugaban majalisar wakilan.

Hakan bai yi wa 'yan majalisa da dama dadi ba, musamman wadanda aka sake zabensu, ciki har da mataimakin shugaban majalisa ta tara Honorabul Ahmed Idris Wase da kuma 'yan majalisar da a yanzu suka janye takararsu.

A sakon da mataimakin shugaban kasar Sanata Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, ya ce 'yan majalisar dokokin biyu sun janye daya yin takara ne bayan sun gana da Shugaba Tinubu.

Ya kara da cewa sun "janye daga takarar shugabancin majalisar dokoki ta 10 sannan suka goyi bayan Honorabul Tajuddeen Abbas."

Shi ma fitaccen dan majalisar dokokin Nijeriya, Honorabul Abdulmumin Jibrin, ya wallafa sako a shafinsa na Facebook cewa 'yan majalisar dokokin biyu sun janye daga takara ne bayan an kwashe tsawon lokaci ana rarrashinsu.

"Bayan an kwashe makonni ana tattaunawa da rarrashi da kuma nuna kwarewar siyasa ta sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, da shawarwarin mataimakin shugaban kasa da ma sanya bakin shugaban kasa, Honorabul Muktar Betara da Yusuf Gagdi sun janye takararsu ta neman zama shugaban majalisa kuma sun goyi bayan Honorabul Tajudeen Abbas," in ji shi.

A cewarsa, hakan ya nuna cewa Tajudeen ba zai fuskanci wata matsala ba wajen zama shugaban majalisar wakilan kasar.

Za a kaddamar da majalisar wakilan, mai mambobi 360, ranar Talatar nan.

TRT Afrika