Tun bayan lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana nade-nade na masu ba shi shawara na musamman takwas, mutane suka fara tambaya da tsokaci game da irin kwarewar da mutanen ke da su.
Bayan Nuhu Ribadu da ya yi suna tun lokacin da ya yi aiki a matsayin shugaban hukumar EFCC, sauran mutum bakwai da Shugaba Tinubu ya nada ba a san su sosai ba.
Mr Dele Alake
Mr Dele Alake shi ne mai ba da shawara na musamman ga Shugaba Bola Tinubu a kan ayyuka na musamman da sadarwa da kuma tsare-tsare.
Alake dai dan Asalin jihar Ekiti ne a kudu maso yammacin Nijeriya, amma ya tashi a jihar Legas inda ya yi karatun digiri na farko da na biyu a Jami’ar Legas.
Ya yi aiki a matsayin edita a gidan rediyo da talabijin na jihar Legas tsakanin shekarar 1980 zuwa 1983.
Daga bisani ya yi aiki a tsohuwar Jaridar Concord daga shekarar 1985 har lokacin da ya yi aiki a matsayin editan Jaridar Sunday Concord.
A fagen siyasa kuma, Mr Dele Alake ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga marigayi MKO Abiola wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a karkashin inuwar jam’iyyar tsohuwar SDP a shekarar 1993.
Tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 ya yi aiki a matsayin kwamishinan labarai da tsare-tsare a gwamnatin Jihar Legas a yayin da Bola Ahmed Tinubu yake gwamna a jihar ta Legas.
Mr Wale Edun
Mr Wale Edun ne Shugaba Tinubu ya nada shi mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kudi.
Dan asalin Jihar Legas ne wnada ya yi kartun digiri na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Landan. Kuma ya yi karatun digirinsa na biyu a kan tattalin arziki a Jami’ar Sussex.
Tsakanin shekarar 1980 zuwa 1986 ya yi aiki a bankin manyan kamfanoni na Chase Merchant Bank.
A shekarar 1986 ya yi aiki da Bankin Duniya a birnin Washington da ke Amurka.
Yana cikin wadanda suka kafa Kamfanin Stanbic IBTC a shekarar 1989, kuma ya zama babban daraktansa.
Ya yi kwamishinan kudi a Jihar Legas tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 a lokacin da Tinubu ke gwamnan jihar.
Mrs Olu Verheijen
Mrs Olu Verheijen da Shugaba Tinubu ya nada a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan makamashi ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga cibiyar inganta samun makamashi ta Energy For Growth Hub.
Ta yi sama da shekara 20 tana aiki a fannin iskar gas da kuma makamashin da za a iya sabuntawa a yankin kudu da saharar Afirka.
Ta yi karatun digiri na farko da digiri na biyu a Jami’ar Long Island da kuma Jami’ar Havard da ke Amurka.
Zachaeus Adedeji
Zachaeus Adedeji da aka nada a matsayin mai ba da shawara na musamman kan kudin shiga ya kwashe shekara 15 yana aiki a matsayin akanta.
Shi ne kwamishinan kudi a jihar Oyo tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 a karkashin gwamnatin marigayi Gwaman Abiola Ajimobi.
Zacheaus ya yi karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife da kuma Jami’ar Havarda da ke Amurka.
Rahatonni dai sun nuna lokacin da ya yi aiki a matsayin kwamishinan kudi a jihar Oyo, jihar ba ta ari ko sisi ba.
Dr Salma Anas Ibrahim
Dr Salma Anas Ibrahim ta fara aiki da ma’aikatar lafiyar tarayyar Nijeriya a shekarar 1999 a matsayin kwararriya a fannin kiwon lafiyar al’umma, kuma aka tura ta mataimakiyar darakta a shirin kawar da cutar HIV/AIDS.
Ita ta fara kafa shirin hana yaduwar kwayar cutar HIV daga uwa zuwa jariri (PMTCT).
Ta yi kwamishiniyar lafiya a Jihar Birno tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
A shekarar 2015 Dr Salma ta koma ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya inda ta jagoranci shirin ba da taimakon kiwon lafiya ga wadanda hargitsi ya rutsa da su.
Sannan ma’aikatar raya yankin arewa maso gabashin Nijeriya da kuma ma’aikatar kare aukuwar bala’i da jin kai sun amafana da shirin.
Dr Salma ta jagoranci shirye-shirye da dama a fannin kiwon lafiya tare da hadin gwiwar kungiyoyi na kasa da kasa irin su hukumar kiwon lafiya ta duniya da sauransu.
Likitar ta yi aiki a matsayin darakta a fannin kiwon lafiyar iyali a ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayyar Nijeriya.
A halin yanzu ita ce darakta a fannin da ke kula da ayyukan asibitoci a ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya inda take kula da gudanarwar duk manyan asibitoci da kuma asibitocin kwararru
Mr. John Ugochukwu Uwajumogu
Mr. John Ugochukwu Uwajumogu shi ne sabon mai ba da shawara na musamman kan Masana'antu da.
Ya kwashe sama da shekara 20 yana aiki a fannin makamashi.
Ya yi karatun digiri na biyu a Jami’ar Tuffs da ke Amurka.
Yau Darazo
Yau Darazo ne Shugaba Tinubu ya nada a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkar siyasa da kuma hulda tsakanin gwamnatoci.
Kafin a nada shi wannan mukamin dai Yau ya yi mai ba da shawara kan ayyuka na musamman ga tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.
Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu ne Shugaba Tinubu ya nada mai a da shawara na musamman kan harkar tsaro.
Dan asalin jihar Adamawa, Nuhu Ribadu ya yi karatun digirinsa na farko da na biyu a fannin shari’ah a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Ya yi aiki a matsayin shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa inda ya yi nasarar kama manyan mutane da laifin wawushe kudin kasa.
Ya nemi shugaban kasar Nijeriya a shekarar 2011 a karkashin Jam’iyyar ACN.