Tajudeen Abbas ya yi aiki a fanni daban-daban kafin a yi aiki ya zama dan majlisa/Hoto:Tajudeen Abbas Twitter

An rantsar da Tajudeen Abbas a matsayin sabon shugaban majalisar wakilai ta 10 ta Nijeriya bayan ya samu kuri'u 353.

Tajudeen ya doke sauran 'yan takara biyu – tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Idris Wase da kuma Sani Jaji, wadanda kowannensu ya samu kuri'u uku kacal.

Sabon Shugaban Majalisar yana wakiltar mazabar Zaria da ke jihar Kaduna wadda ke shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya kuma dan jam'iyya mai mulki ta APC ne shi.

An zabe shi ne tare da mataimakinsa Benjamin Kalu, mai shekara 52, wanda ya fito daga jihar Abia da ke kudu maso gabashin Nijeriya.

Tajudeen, wanda tsohon malamin jami'a ne, ya fara zuwa majalisar ne a shekarar 2011.

Kuma shi ne dan takarar da jam'iyyar mai mulki ta APC ta umarci mambobinta da ke majalisar su zaba a matsayin shugaban majalisar wakilan kasar ta 10 a ranar Talata.

Tajudeen Abbas ya yi koyarwa a makarakar firamare da ma makarantun gaba sakandare

An haifi Tajudeen Abbas a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1963 a unguwar Kwarbai a Zaria da ke jihar Kaduna. Dan gidan sarauta ne a Masarautar Zazzau kuma yanzu haka yana rike da sarautar Iyan Zazzau.

Ya yi karatu a kwalejin horar da malamai ta Kaduna Teachers College (KTC) inda ya samu shaidar Teachers Grade II Certificate a shekarar 1981.

Daga bisani ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, inda ya yi digirinsa na farko da na biyu, ya karanta harkokin Kasuwanci wato Business Administration.

Haka zalika ya yi digirinsa na uku a wannan fannin amma a Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.

Ya fara koyarwa a makarantar firamare kodayake daga baya ya koma koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha.

Bayan haka kuma ya yi aiki a kamfanin taba na Nigerian tobacco Distribution Company a matsayin manajan kasuwanci.

Tuni dai Abbs Tajudeen ya fara jagorancin majalisar wakilan Nijeriya bayan ya sha rantsuwa/Hoto:bidiyo:Arise

Sabon shugaban majalisar ya shiga harkokin siyasa ne a shekarar 2010, kuma an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta Nijeriya a shekarar 2011.

Tsohon malamin makarantar ya gabatar da kudurorin dokoki da dama kuma ya kasance mamba kwamitoci majalisar da dama ciki har da kwamitin kudi da na tsaro da na tsare-tsaren kasa.

Kafin zaben jagorancin majalisar a farkon makon nan, Tajuddeen ya kasance shugaban kwamitin sufuri a tudu (wato Chairman for Land Transport) a majalisa ta tara.

TRT Afrika