Sanata Kyari ya taba wakiltar Arewacin Borno a majalisar dattawan Nijeriya tsakanin 2015 zuwa 2019./Hoto:OTHER

Mataimakin shugaban APC mai mulkin Nijeriya shiyyar arewacin kasar Sanata Abubakar Kyari ya zama sabon shugaban jam'iyyar na rikon kwarya.

Kyari ne da kansa ya sanar da nadin nasa ranar Litinin a Abuja yayin da ya jagoranci taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar.

Ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu da sakatarenta Iyiola Omisore sun ajiye mukamansu.

A cewarsa, mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa Festus Fuanter, zai rike mukamin sakataren jam'iyyar na riko.

A yanzu sabon shugaban APC ya daga taron shugabannin jam'iyyar da a baya aka shirya yi ranar Talata da Laraba, 18 da 19 ga watan Yuli.

Sanata Kyari gogaggen dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama.

Ya taba wakiltar Arewacin Borno a majalisar dattawan Nijeriya tsakanin 2015 zuwa 2019.

TRT Afrika