A yayin da aka cika shakara 10 da sace ƴan matan makarantar Chibok 276 a jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, iyayen sauran matan da har yanzu ba a gan su ba sun bayyana halin ƙuncin da suke ciki tare da jaddada kiransu ga gwamnatin aƙsar ta kuɓutar da ‘ya’yansu.
Sun yi kira ne a yayin taron da ƙungiyar 'Bring Back Our Girls (BBOG), wadda ke fafutukar ganin an kuɓutar da 'yan matan, ta gudanar a dandalin UNITY Fountain da ke Abuja babban birnin ƙasar.
A wani sako da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta yi wa gwamnati Nijeriya tuni kan hakkinta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
''A ci gaba da gangaminmu, muna daɗa kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan ta mayar da hankali wajen tabbatar da ganin an dawo da sauran 'yaƴanmu mata da aka sace '' in ji sanarwar.
''Shekara 10 ta yi nisa kuma mun yi haƙuri da sosai'' a cewar Dauda Iliya, Shugaban Al'ummar "Kibaku" da ke Chibok yana mai ƙarawa da cewa ''Iyaye 48 sun mutu tun bayan sace ƴaƴansu da aka yi sannan ƴan ta'adda sun kashe iyaye uku''.
Har yanzu akwai aƙalla mata 90 da ba a gano inda suke ba duk da rahotanni sun yi nuni da cewa tun da farko 57 daga cikin 276 sun gudu daga dajin Sambisa da ke da tazarar Kilo mita 60 daga Kudu maso yammacin Maiduguri inda aka kai su.
Kazalika 107 sun kuɓuta a 2018, sannan an kuɓutar da ƙarin da wasu a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022.
An kuma yi nasarar ɗaukar nauyi wasu daga cikin ƴan matan da su ka kuɓuta daga hannun 'yan ta'addan na Boko Haram don ci gaba da karatu har zuwa Turai.
Kazalika akwai waɗanda har yanzu ke hannun sojoji da mazajen su 'yan Boko Haram ne da su ka tuba.
Har yanzu dai wasu daga cikin iyayen matan ba su fid da da rai sake haduwa da ƴayansu ba amma tuni wasu sun hakura.
Satar ƴan matan daga makarantarsu ta sakandare da ke Chibok a shekara ta 2014 ya haifar da takaici a tsakanin masu sharhi da ma wasu ƙasashen duniya.