A ranar Lahadi ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali suka sanar da ficewa daga ECOWAS. / Hoto: Reuters

Tun bayan da ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali suka sanar da aniyarsu ta ficewa daga ECOWAS, jama’a da dama ke ta ce-ce-ku-ce dangane da hakan inda wasu ke tambaya ko shin ƙasashen suna da damar ficewa daga ƙungiyar a duk wani lokaci da suke so.

Tun bayan kafa ECOWAS a 1975, akwai yarjejeniya a rubuce wadda ta zama dokar gudanarwar ƙungiyar bayan shugabannin ƙasashen ƙungiyar 16 sun saka mata hannu, inda aka sake sabunta yarjejeniyar a shekarar 1993 inda shugabannin ƙasashen ƙungiyar waɗanda suka zama 15 daga baya suka saka mata hannu.

Yarjejeniyar ta tanadi abubuwa da dama da suka shafi tsare-tsare da dangantaka da kuma yadda za a gudanar da ayyukan ƙungiyar.

Babbar tambayar da jama’a suka fi yi a halin yanzu ita ce ko akwai matakai da aka tanada kafin ficewa daga ECOWAS?

A cikin sashe na 91 na kundin yarjejeniyar ECOWAS ta 1993, an tanadi wasu hanyoyi da ƙasa mambar ƙungiyar za bi kafin ficewa.

“Duk wata ƙasa mamba da ke son ficewa daga ƙungiyar za ta bayar da sanarwa a rubuce ga Babban Sakataren ƙungiyar shekara guda kafin ficewar, wanda shi kuma zai shaida wa jihohi mambobi.

“Zuwa lokacin da wa’adin zai kawo ƙarshe, idan ba a janye kudirin ba, ƙasar za ta kasance ta fita daga ƙungiyar,” kamar yadda yarjejeniyar ta ce.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa a cikin shekara ɗaya da bayar da wannan sanarwar, akwai buƙatar ƙasar da ke son ficewar ta ci gaba da bin dokoki da tsare-tsaren ƙungiyar kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Bijire wa ECOWAS

Tun bayan juyin mulki na baya-bayan nan da aka yi a Nijar wanda aka hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum, ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali suka ƙara haɗa kansu tare da bijire wa ECOWAS.

Duka ƙasashen uku sojoji ne ke mulkinsu bayan sojojin sun yi wa gwamnatocin farar hula juyin mulki, dalilan da ya sa kenan ECOWAS ɗin ta saka musu takunkumai.

An ta ƙoƙarin sulhu tsakanin ƙasashen da ECOWAS sai dai abin ya ci tura.

Bayan haka ƙasashen sun ƙulla ƙawancen Sahel Alliance ko kuma Liptako-Gourma wadda wasu ke kallo tamkar kishiya ce ga ECOWAS.

Ƙasashen sun ce wannan yarjejeniyar da suka yi za ta mayar da hankali wurin ci-gabansu ta fannin tsaro da tattalin arziki.

TRT Afrika