Bayan lura da matsananciyar matsalar jinƙai a yankin Sahel da Tafkin Chadi a Yammacin Afirka, hukumomi a Saudiyya sun sanar da taron ƙoli na ministoci don neman tallafin jin-ƙai ga al'ummar yankin.
Taron na haɗin gwiwa ne da Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi, OIC, da Cibiyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Harkokin Jinƙai, OCHA, da ta Kwamishinan Majalisar Ɗinkin Duniya kan 'Yan gudun Hijira, UNHCR.
Wata sanarwar da aka fitar ranar Juma'a 23 ga Agusta daga hukumar jinƙai ta Saudiyya, wato Cibiyar Sarki Salman don Jin-kai, ta ce ƙasar za ta shirya taron masu ba da tallafin ranar 26 ga Oktoban 2024.
Manufar taron shi ne tattaro tallafi da hanyoyin taimakawa al'ummar da suka tagayyara, da kuma 'yan gudun hijira a yankin Sahel da ke fama da ƙalubale daban-daban.
Yunƙurin taron shi ne tallafawa don ceto rayuka, kare farar-hula, da ɗaukaka ƙoƙarin mutanen da rikice-rikice suka shafa. Ƙasashen Yankin Sahel da Tafkin Chadi suna fama da tsanantar tarin matsaloli cikin shekaru 10 da suka wuce.
Waɗanda za su ci gajiyar tallafin sun haɗa da al'ummar da ke cikin mawuyacin hali a Nijeriya, Nijar, Chadi, Kamaru, Burkina Faso, da Mali.
Sanarwar ta bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa kusan mutane miliyan 33 suna buƙatar taimako da kariya a faɗin yankin, ciki har da mutane miliyan 11 da aka raba da matsugunansu, da 'yan gudun hijira a yankin Sahel da Tafkin Chadi.
Baya ga rashin tabbas a yankin, kama daga na zamantakewa da tattalin arziƙi, akwai matsalar ƙafewar Tafkin Chadi, wanda ke tallafa wa rayuwar miliyoyin jama'a. Hakan ne ya sa ake buƙatar taimakon gaggawa ga yankin.
Shugaban hukumar jinƙai ta Saudiyya, Dr. Abdullah Al Rabeeah ya yi kira ga ƙasashen OIC da cibiyoyin jin-ƙai su bayar da tallafin kuɗi don kyautata lamura ga al'ummomin yankin.