Likitocin da ke kula da mahajjatan Nijeriya da ke Saudiyya sun bayyan cewa zuwa yanzu sun gano masu larurar kwakwalwa 30 da kuma mata masu ciki bakwai a garuruwan Makkah da Madinah.
Shugaban likitocin da ke kula da Alhazan Nijeriya Dakta Usman Galadima ne ya bayyana haka a wani taron bita kan hawan Arafat da Hukumar Alhazan Nijeriya ta gudanar a garin Makkah a ranar Asabar.
Jaridar PR Nigeria ta ruwaito shi yana cewa tuni aka kula tare da yin magani ga mutum talatin din da aka gano suna da larurar ta kwakwalwa sa’annan an tabbatar da cewa za su iya ci gaba da gudanar da Aikin Hajjinsu.
Sa’annan ya ce daga cikin mata masu juna biyu akwai daya wadda ta haihu ta hanyar yi mata tiyata sa’annan daya kuma ta yi barin cikin sakamakon gwagwarmaya da dawainiya da ke tattare da Aikin Hajji.
Ya kuma lissafo cewa daga cikin masu juna biyun, akwai biyu wadanda suka fito daga Jihar Sokoto sa’annan jihohin Katsina da Yobe da Adamawa da Kwara da Filato aka samu daya daga kowanensu.
Dakta Galadima ya ce a bana an samu adadi mai yawa na masu ciki da wadanda suka tsufa da masu tsananin rashin lafiya wadanda bai kamata su hau jirgi ba wanda hakan na nufin ba za su iya Aikin Hajji ba.
Ya bukaci jihohin Nijeriya kan cewa su kara tsauri wurin tantance maniyyata domin tabbatar da cewa ba a bar masu ciki da tsofaffi da wadanda suke da wani ciwo mai barazana ba su tafi Aikin Hajji ba.