'Yan kasar Nijar sun kwashe wata da watanni suna gudanar da zanga-zangar kyamar Faransa da neman ta kwashe dakarunta daga kasar./Hoto: Reuters

Gwamnatin sojin Nijar ta ce a yau Talata rukunin farko na sojin Fasansa zai soma ficewa daga kasar.

Sanarwar na zuwa ne a yayin da Algeria ta yanke shawarar "dage" shirinta na shiga tsakani kan yadda za a shawo kan matsalar da Nijar ta fada a ciki.

"Jami'an tsaronmu za su soma raka rukunin farko (na sojojin Faransa) da zai fita daga kasar a ranar (Talata)," a cewar sanarwar da aka karanta a gidan talbijin na kasar.

Sanarwar ba ta yi karin bayani game da inda sojojin za su nufa ba.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yuli ne suka bukaci Faransa ta kwashe dakarunta 1,400 da ke kasar.

A watan jiya shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda a baya yake dasawa da gwamnatin da aka hambarar, ya ce zai kammala kwashe dakarunsa daga Nijar "nan da karshen shekarar da muke ciki".

Faransa ta jibge sojojinta a Nijar ne domin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda da ke da alaka da Al Qaeda da Islamic State a yankin Sahel.

Bayan an gudanar da wani taro da kuma "yin musayar bayanai tsakanin gwamnatinmu da hukumomin Faransa, an amince da jadawalin kwashe dakarun kasar cikin lumana", in ji sanarwar ta ranar Litinin.

A karshen makon jiya, an ga jerin gwanon motoci a arewa maso yammacin kasar da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali inda sojojin Faransa 400 suke, da kuma wasu sojojin da ke Yamai, a cewar wasu majiyoyin tsaro na Nijar da Faransa.

An amince akalla tawaga biyu ta je sansanin sojojin Faransa da ke Ouallam da Tabarey-Barey inda ake sa rai za a kwashi sojojin wuraren domin kai su Yamai.

Dakarun Faransa sun fada cikin halin rashin tabbas tun bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka umarci su fice daga kasar, inda ba sa samun isasshen abinci sannan dubban 'yan Nijar sun yi wa sansaninsu tsinke suna neman su fita daga kasar.

Dakarun na Faransa suna da zabi biyu ne na fita daga Nijar - ko dai ta kasar Benin -- ko kuma ta Chadi saboda Nijar ta haramta wa jiragen Faransa shiga sararin samaniyar kasar.

Faransa ta kara yawan dakarunta a Nijar bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun kore ta daga can, inda ta aika karin jiragen helikwafta da jirage marasa matuka da jiragen yaki.

AFP