Sarkin da sarauniyar sun isa filin saukar jirage na kasa da kasa na Jomo Kenyatta a babban birnin kasar Kenya Nairobi da misalign karfe 11 na dare ranar Litinin.
Sakataren harkokin wajen Kenya Musalia Mudavadi ne ya tarbi sarkin da sarauniyar.
Jakadan Birtaniya a Kenya, Neil Wigan, ya kasance a filin jiragen saman yayin da jirgin masarautar Birtaniya ya sauka.
Rangadin sarkin da sarauniyar a Kenya ita ce ziyara a hukumance ta farko da Sarki Charles da Sarauniya Camilla suka kai wa wata kasar Afirka, kuma ziyararsu ta farko zuwa daya daga cikin kasashe renon Ingila tun bayan bikin nadin sarautarsu a watan Mayun shekarar 2023.
Rashin adalcin mulkin-mallaka
Ana sa ran za su gana da iyalan shugaban kasar Kenya su kuma gana da ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a fagen fasaha kuma su zaga birnin Mombasa da ke bakin teku, kamar yadda fadar Buckingham ta bayyana.
Ana sa ran sarkin ya yi tsokaci kan batun rashin adalci na lokacin da Birtaniya take yi wa Kenya mulkin-mallaka.
Masu sarautar suna kasar Kenya ne a wata ziyara ta kwanaki hudu daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa ranar uku ga watan Nuwamba.