Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta sallami sanannun ministocinta biyu a wani ɓangare na garambawul ga majalisar zartarwa, kamar yadda daraktar riƙo ta sashen sadarwar fadar shugaban ƙasa, Sharifa Nyanga ta bayyana.
Korar Ministan Harkokin Waje January Makamba da Ministan Sadarwa, Yaɗa labarai da Fasahar Sadarwa, Nape Nnauye na zuwa a yayin da ake yaɗa jita-jitar suna yin wani yunƙuri cikin sirri na ƙalubalantar sake zaɓar Samia. Shugaba Samia ta hau kan mulki bayan rasuwar Shugaba John Magafuli.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnati Moses Kusiluka ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana Mahmoud Thabit Kombo, ɗan majalisar dokoki a matsayin Ministan Harkokin Waje da Ƙawancen Gabashin Afirka. Kafin wannan muƙami, Kombo ne jakadan Tanzania a Italiya.
Sanarwar ta ce Jerry Silaa zai maye gurbin Nnauye a matsayin Ministan Sadarwa, Yaɗa Labarai da Fasahar Sadarwa. A baya Silaa na riƙe da muƙamin Ministan Ƙasa, Gidaje da Tsugunar da Jama'a.
An naɗa Deogratius John Ndejembi a matsayin sabon Ministan Ƙasa, Gidaje da Tsugunar da Jama'a. Kafin naɗin nasa, shi ne Ƙaramin Minista a ofishin Firaminista.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an naɗa Ridhiwani Kikwete a matsayin Ƙaramini Minista a ofishin Firaminista. Kafin naɗin nasa, Kikwete ya yi aiki a matsayin Mataimakin Minista a sashen Ayyukan Gwamnati na Ofishin Shugaban Ƙasa.
Cosatto Chumi ya zama sabon Mataimakin Ministan Harkokin Waje, inda ya maye gurbin Mabrouk Nassor Mabrouk, wanda aka bai wa wani sabon muƙamin.
An naɗa Deus Clement Sangu a matsayin Mataimakin Minista a sashen kula da ingancin ayyukan gwamnati na ofishin Shugaban Ƙasa.
Dennis Lazaro Londa ya zama Mataimakin Firaministan Harkokin Waje da Ƙawancen Gabashin Afirka, wanda ya maye gurbin Stephen Lujwahuku Byabato, wanda aka sauke daga muƙaminsa.
Kazalika shugabar ƙasar ta yi wa wasu manyan jami'an gwamnatin sauyin wuraren aikin waɗanda suka haɗa da manyan sakatarori, shugabannin gundumomi, inda Eliakim Chacha Maswi ya zama Babban Sakatare a Ma'aikatar Harkokin Kundin Tsarin Mulki da Shari'a, sai Mary Gaspar Makondo da aka naɗa a matsayin Sakatariyar Gwamnatin Yankin Ruvuma.
Garambawul ɗin na nufin nuna ƙarfin ikon shugabar a yayin da ake tunkarar zaɓe a Tanzania a shekara mai zuwa.