El-Rufai da Badaru da Wike su ne tsofaffin gwamnonin Kaduna, Jigawa da Ribas.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai da takwaransa na Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar suna cikin mutanen da Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya aika sunayensu ga Majalisar Dattawan kasar don neman amincewarta ya nada su mukamin ministoci.

Shugaban majalisar ta dattawa Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman da majalisar ta yi ranar Alhamis.

Kazalika tsohon gwamnan Jihar Ribas Ribas Nyesom Wike da takwaransa na Jihar Ebonyi Dave Umahi su ma suna cikin jerin mutanen da aka nada a mukamin na ministoci.

Sauran mutanen su ne:

Muhammad Ali Pate

Hannatu Musawa

Bello Mohammed Goronyo

Sani Abubakar Danladi

Abubakar Momoh

Lateef Fagbemi

Yusuf Maitama Tukur

Nkiru Onyejiocha

Olawale Edun

Mohammed Dangiwa

Stella Okotete

Uche Nnaji

Betta Edu

Doris Uzoka

Ekperikpe Ekpo

Olubunmi Ojo

Uju Ohaneye

Mohammed Idris

Wahid Adelabu

Iman Suleiman Ibrahim

Joseph Utsev

Abubakar Kyari

John Enoh

Sani Abubakar Danladi

TRT Afrika