Matashiyar ‘yar siyasar nan ta Nijeriya wadda Shugaba Tinubu ya bai wa mukamin minista Maryam Shetty ta bayyana cewa kaddara ce ta sa ya amshe mukamin da ya ba ta.
Ta bayyana haka ne a wani sakon da ta wallafa a shafin Facebook inda ta ce a yayin da wasu suke daukar wannan a matsayin wani koma baya amma imaninta a matsayinta na Musulma ya sa ta dangana.
“Ina daukarsa a matsayin hukuncin Allah, wanda na yi imani kan cewa shi ke bayar da mulki a lokacin da ya so, shirinsa a kowane lokaci a gaban namu yake,” in ji ta.
Sakon nata na zuwa ne kwana guda bayan da Tinubu ya musaya sunananta da Dakta Mariya Mairiga Mahmoud Bunkure.
Duk da sauya sunanta da Tinubun ya yi cikin gaggawa, Maryam ta gode wa shugaban kan zabarta da ya yi da farko.
“Duk da wannan sauyin na ba tsammani, ina godiya ga Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya zabe ni domin rike wannan babban mukamin. Ba a nan tafiyar ta tsaya ba; Ina ganin wannan a matsayin somin tabi, mafi alkhairi na nan tafe,” in ji ta.
“Ina so na tabbatar wa magoya bayana cewa ba wannan ne karshe ba, farkon sabon babi ne, ina bukatar dukanmu da mu ci gaba da yin addu’o’i ga kasarmu da kuma goyon baya ga shugaban kasarmu a daidai lokacin da yake so a kawo ci gaba ga Nijeriya,” in ji Maryam Shetty.
Kafin Shugaba Tinubu ya musaya sunan Maryam Shetty, an ta tattauna kan batun bata minista a shafukan sada zumunta inda wasu suka nuna goyon bayansu dari bisa dari wasu kuma suka rinka Allah wadai da lamarin.
Shugaba Tinubun dai bai bayyana dalilin da ya sa ya janye sunanta daga majalisar dattawan domin tantance ta ba.
Rahotanni sun ce ita kan ta Maryam Shetty labarin ya riske ta tana harabar Majalisar Dattawan Nijeriya a lokacin da take tare da magoya bayanta domin tantance ta.