Shugaba Tinubu ya nada Atiku Bagudu, Bello Matawalle, Simon Lalong da karin mutum 16 ministoci

Shugaba Tinubu ya nada Atiku Bagudu, Bello Matawalle, Simon Lalong da karin mutum 16 ministoci

Tsoffin gwamnoni biyar na cikin mutanen da shugaba Tinubu ya mika wa majaliasar dattawan Nijeriya domin tantance su don zama ministoci
Bagudu ya rike mukamin gwamnan jihar Kebbi daga 2015 zuwa 2023./Hoto: Shafin Facebook na Atiku Bagudu da Matawalle da Shety

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike wa da majalisar dattawan kasar sunayen tsoffin gwamnonin jihar Kebbi, Zamfara, Filato, Osun da Yobe domin ya nada su a mukaman ministoci.

Shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman majalisar na yau Laraba.

Tsoffin gwamnonin na cikin karin mutum 19 da Shugaba Tinubu ya aike da sunayensu domin a tabbatar da su a mukamin ministoci.

Tsoffin gwamnonin su ne Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Bello Matawalle na jihar Zamfara, Simon Lalong na jihar Filato da Ibrahim Geidam na jihar Yobe da Adegboyega Oyetola na jihar Osun.

Sauran su ne:

Abdullahi Tijjani Gwarzo

Bosun Tijjani

Dr Maryam Shetti

Ishak Salako

Alkali Ahmed

Dr Tunji Alausa

Yusuf Tanko Sununu

Lola Adejo

Shua’ibu Abubakar Audu

Tahir Mamman

Sanata Aliyu Sahabi Abdullahi

Sanata Heineken Lokpobiri

Uba Maigari

Zephaniah Jisalo

TRT Afrika