Alƙaluma sun nuna cewa yaƙin Sudan ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 16,000 sannan ya raba fiye da mutum miliyan 2 da gidajensu inda suke gudun hijira a Chadi, Masar, Ehiopia da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. / Hoto: Reuters

Sabon gumurzu ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces [RSF] a birnin el-Fasher na Jihar North Darfur, a cewar masu fafutuka na ƙasar Sudan.

"An yi ta musayar harbe-harbe da igwa da manyan makamai tsakanin sojojin Sudan da rundunar Rapid Support Forces," in ji wata sanarwa da ƙungiyar El-Fasher Resistance Committee ta fitar ranar Juma'a.

Sanarwar ta ƙara da cewa "luguden wutar da aka riƙa yi da igwa ya faɗa gidajen jama'a, lamarin da ya jikkata mutane da dama."

Har yanzu rundunar sojojin Sudan da dakarun RSF ba su ce komai game da sanarwar ba.

Yaƙi ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu ne tun watan Afrilun shekarar 2023.

El-Fasher shi ne babban birnin Jihar North Darfur, wacce ke tsakiyar lardin Darfur kuma shi ne kaɗai birnin da dakarun RSF ba su ƙwace ba.

Ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya sun ƙara ƙaimi wurin kiraye-kirayen da suke yi don tsagaita wuta a yaƙin Sudan inda ake fargabar cewa miliyoyin mutane na dab da faɗawa cikin bala'n yunwa sakamakon rashin abinci da yaƙin ya haddasa.

An kashe dubban mutane, an raba miliyoyi daga muhallansu

Yaƙin Sudan ya ɓarke ne ranar 15 ga watan Afrilun 2023 sakamakon saɓanin da aka samu tsakanin shugaban rundunar sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al Burhan da tsohon mataimakinsa kuma shugaban rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces [RSF] Mohamed Hamdan Dagalo.

Alƙaluma sun nuna cewa yaƙin ya yi sanadin mutuwa fiye da mutum 16,000 sannan an raba kusan mutum miliyan biyu da muhallansu, inda suka tsare zuwa maƙwabtan ƙasashe irin su Chadi, Masar, Ethiopia da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Kusan mutum miliyan 8.5 ne suke gudun hijira a cikin ƙasar.

Har yanzu an kasa yin sulhu tsakanin ɓangarorin biyu duk da shiga tsakanin da Saudiyya da Amurka suka kwashe tsawom lokaci suna yi.

TRT Afrika da abokan hulda