Lamarin ya faru ne a yankin Yammacin Ghana a ranar Talata. / Hoto: GNA

Rundunar Sojin Saman Ghana ta ce ta soma gudanar da bincike bayan wani jirginta mai saukar ungulu ya yi hatsari a Yammacin ƙasar.

Rundunar sojin saman ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata da maraice.

Ta ce jirgin mai lamba GHF 696 ya yi saukar gaggawa a ƙauyen Bonsukrom da ke kusa da Agona Nkwanta sakamakon rashin yanayi mai kyawu da misalin 12:30.

Jirgin yana ɗauke da fiye da mutum ashirin waɗanda suka haɗa da sojoji da ma'aikatan Kamfanin Gas na Ghana.

Wani bidiyo da aka yaɗu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jirgin ya tunkari wani filin ƙwallo a ƙauyen inda ya yi yunƙurin saukar gaggawa amma daga baya ya kife.

“A lokacin da lamarin ya faru, jirgin mai saukar ungulu na ɗauke da fasinjoji 21 da suka ƙunshi ma’aikatan Kamfanin Gas na Ghana da ma’aikatan jirgin waɗanda suke gudanar da bincike a kan bututun da ke cikin ruwa na matatar gas ta Atuabo,” in ji sanarwar.

Rundunar sojin ta ce duka fasinjojin da ke cikin jirgin na nan lafiya ƙalau.

Sai dai ta ce a halin yanzu ana gudanar da gwajin lafiya a kansu haka kuma an soma bincike domin gano musabbabin saukar gaggawa da jirgin ya yi.

TRT Afrika