Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayar da umarnin binciken duka wuraren da soji ke tsare mutane

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kaddamar da binciken da ya dace domin gano sahihancin zargin da aka yi a wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda wasu ma’aikatan da ke tsare a gidan yari na 8 Division Garrison da ke Sokoto suka shirya.

Haka kuma rundunar ta ce za ta aiwatar da umarnin da Shugaban Sojin Nijeriya Janar Taoreed Lagbaja ya bayar na binciken duka wuraren da soji ke tsare mutane

A kwanakin baya ne wasu jaridun Nijeriya suka ruwaito yadda aka harbi wani kofur ɗin soja bayan wasu sojoji sun fito daga gadirum ɗin da ake tsare da su a Sokoto inda suka yi zanga-zanga kan rashin abinci mai kyau da wurin kwana.

Da yake mayar da martani a ranar Asabar, Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya nuna rashin jin daɗinsa kan faruwar lamarin, haka kuma ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta amince da yadda waɗanda ke tsare suka bayyana kokensu ba.

Ya ce, “bore da tayar da hankali ga hukuma babban laifi ne, kuma wannan lamarin ya nuna irin haka.

“Don haka, a gefe guda, sojoji, sun ci gaba da aiwatar da umarnin shugaban soji na duba halin da ake ciki na duka wuraren da sojoji ke tsare mutane, sakamakon rayuwar waɗanda ake tsare da ita na da muhimmanci.

"Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta sojojin da ke da hannu a cikin lamarin. Halayyar rashin da'a a gadirum ɗin Sokoto na rashin cika dukkan hanyoyin da ake da su na mika kokensu ga hukumomin da suka dace kuma idan aka gano sun yi ba a yi komai ba, za a dauki matakan da suka wajaba a kan duk wanda aka samu ya kasa gudanar da ayyukansa yadda ya kamata," in ji sanarwar.

TRT Afrika