Binciken wucin-gadi da aka gudanar ya nuna cewa sun fito daga garuruwa daban-daban na Nijeriya domin zuwa Tafkin Chadi kamun kifi. / Hoto: MNJTF

Dakarun rundunar sojin haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ta MNJTF reshen Diffa a Jamhuriyar Nijar ta kama ‘yan Nijeriya 174 majiya ƙarfi waɗanda ke ƙoƙarin tsallakawa cikin Nijar.

Rundunar ta MNJTF ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar inda ta wallafa hotunan tarin mutanen da aka kama.

Rundunar ta ce ta kama ayarin jama’ar ne sakamakon tana sane da tasirin irin wannan tafiyar tasu, inda nan take ta soma gudanar da bincike domin tabbatar da cewa ba su da wata illa ga tsaron yankin.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar, ya bayyana cewa an kama mutanen ne a Gueskeru wadda iyaka ce mai muhimmanci wadda ke haɗa Jihar Yobe da Jamhuriyar Nijar.

Binciken wucin-gadi da aka gudanar ya nuna cewa sun fito daga garuruwa daban-daban na Nijeriya domin zuwa yankin Tafkin Chadi kamun kifi.

A ‘yan kwanakin nan ne aka samu rahotannin ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa waɗanda rahotanni ke cewa sun shiga Nijeriya ne daga makwabtan ƙasar.

Hakan ne ma ya sa jami’an tsaron ƙasar suka lashi takobin fatattakar Lakurawan da kuma magance duk wata barazana a ciki da wajen ƙasar.

TRT Afrika