Ayyukan ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun ƙaru, wanda hakan ke ƙara jawo taɓarɓarewar tsaro wanda masana daga Majalisar Ɗinkin Duniya ke ganin ya samo asali ne daga Sudan mai maƙwabtaka.
Masanan sun ruwaito sahihan rahotanni waɗanda ke cewa sojojin Sudan sun rinƙa kai hari ta samu a wuraren da ke da iyaka da inda mayaƙan abokan gabarsuna RSF suke, inda suke tsallakawa domin ɗaukar wasu daga cikin masu riƙe da makamai na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka aiki.
Sudan ta faɗa cikin rikici a tsakiyar Afrilun 2023, tun bayan da aka soma samun rashin jituwa tsakanin sojojin na Sudan da RSF a Khartoum.
Rikicin ya bazu zuwa wasu yankuna da suka hada da Darfur mai iyaka da yankin Vakaga na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka a arewa maso gabashin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 14,000 ne aka kashe tare da jikkata 33,000 a yakin Sudan.
Tsallaka iyaka domin tserewa
Kwamitin kwararru da ke sa ido kan takunkumin da aka kakaba wa sojojin haya da masu dauke da makamai a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa 'yan gudun hijirar Sudan kusan 10,700 rajista wadanda suka tsallaka kan iyaka zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a karshen watan Maris.
Yakin da ake yi a Sudan ya kuma katse muhimmiyar hanyar kasuwanci da sufuri tsakanin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da yankin Darfur na Sudan ta kan iyakar Am Dafok.
Lamarin ya sa mutane a Vakaga da makwabciyarta Haute-Kotto cikin rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata, kuma isar da kayayyakin agaji ya kasance a hankali da tsada, in ji kwamitin.
Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta kasance daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya duk da dimbin arzikin ma'adinai da suka hada da zinari da lu'u-lu'u da take da su.
Ayyukan ‘yan tawaye da suka ƙi ƙarewa
Kungiyoyin 'yan tawaye sun gudanar da ayyukansu ba tare da wani hukunci ba a fadin kasar cikin shekaru goma da suka gabata, inda suka dakile aikin hako ma'adinai da kamfanonin kasashen waje ke yi.
Kasar dai ta fada cikin rikici tun shekara ta 2013, lokacin da ‘yan tawaye suka kwace mulki tare da tilasta wa shugaban kasar Francois Bozize na wancan lokaci ya sauka daga mulki.
Masanan sun ce a ranar 10 ga Disamba, 2023, an ji karar fashewar wasu abubuwa guda shida a sansanin masu horarwa na Rasha da ke Kaga Bandoro a yammacin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kuma masu horarwa uku ne suka mutu tare da jikkata mutane bakwai.