Sudan

Dubban mutane ne ke tserewa daga Khartoum, babban birnin Sudan yayin da aka shiga kwana na biyar ana fafatawa tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF.

An ci gaba da jin karar fashewar abubuwa a birnin ranar Laraba.

Fararen-hula da suka makale a gidajensu sun kasance cikin mawuyacin yanayi sakamakon cigaba da rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar cewa kusan mutum 200 sun rasa rayukansu sakamakon arangamar.

Shugabannin kasashen Kenya, Djibouti da Sudan ta Kudu sun dakatar da shirinsu na zuwa Sudan domin sulhunta bangarorin biyu.

Ranar Talata Kwamandan Rundunar Rapid Support Forces [RSF], Mohamed Hamdan Dagalo ya ce zai amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa'a 24.

Sai dai rundunar sojin kasar ta ce ba ta da masaniya a kan hakan, kuma daga baya ta zargi RSF da yin karya.

Tuni Rundunar RSF ta soki gwamnatin da karya yarjejeniyar.

Da misalin karfe 4 na yamma agogon GMT, lokacin da ya kamata yarjejeniyar da aka ce an cimma ta fara aiki, an rika jiyo karar harbe-harbe a Khartoum, kamar yadda shaidu da yawa suka fada, kuma an ci gaba da jin hakan har zuwa dare.

"Har zuwa yanzu ana ci gaba da yaki a Sudan, ciki har da birnin Khartoum da sauran wurare. Babu alamar kawo karshen fadan," a cewar mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

Dagalo ya sanar da batun yarjejeniyar ce bayan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya yi magana da janar-janar din biyu inda "ya nemi a yi gaggawar tsagaita wuta."

Ministocin Harkokin Wajen Kasashe Bakwai Masu Karfin Tattalin Arziki na G7, wadanda suka hada da Amurka, su ma a ranar Talata sun yi kira ga bangarorin biyu masu fada da juna da su yi gaggawar dakatar da yakin, a yayin da ake jin kararrakin fashewar abubuwa a Khartoum, inda mayakan sa kai masu rawani ke ta sintiri a kan titunan birnin.

Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, kan hanyoyin da za a bi a dakatar da fadan tare da kwantar da hankula a Sudan.

Amurka ta ce an bude wa wata tawagar jami'an diflomasiyyarta wuta sannan kuma an kai wa jakadan Kungiyar Tarayyar Turai hari a gidansa.

Kungiyoyin bayar da agaji sun ce ana ta satar kayayyakin kula da lafiya da sauran kayan agaji.

Akwai fargabar cewa rikicin ka iya bazuwa zuwa sauran sassan kasar ta hanyar kai hare-haren sama.

Ganau sun ce an girke manyan motoci masu dauke da bindiogin kakkabo jiragen sama a unguwannin mutane a Khartoum tun da safiyar ranar Talata.

An farfasa gilasai da tagogi na gidajen mutane da ofisoshi da dama a fadin birnin.

TRT World