Akalla mutum hudu suka samu munanan raunuka sakamakon rikicin da aka yi tsakanin wani soja da dan sanda a Jamhuriyyar Nijar.
Lamarin ya faru ne a kasuwar Dolé da ke Zinder inda har ta kai ga dan sanda ya harbi soja da bindiga, kamar yadda jaridar ActuNijar ta ruwaito.
Rikicin ya fara ne a lokacin da wani soja yake so ya shiga kasuwar da babur dinsa, sai dan sandan da ke aiki a wurin ya umarce shi da ya ajiye babur din a waje sakamakon an hana shiga da babur cikin kasuwa.
Daga nan ne rikici ya kaure bayan sojan ya sharara wa dan sandan mari wanda hakan ya sa jama’a suka shiga suka raba fadan.
Shaidu sun bayyana cewa rikicin ya dauki sabon salo ne bayan sojan ya tafi ya dawo ya dauki gilashinsa sai dan sandan ya dauki bindigarsa ya harbi sojan a idonsa na dama.
Rahotanni sun ce baya ga sojan, akwai wani mutum da aka harba a hannu wani kuma aka harbe shi a cinya sai kuma wata mata da ta je siyayya aka harbe ta a gwiwa.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce sai da dan sandan ya yi sama da minti 30 da bindigarsa a hannu kafin dakarun jandarma suka isa wurin suka kama shi.
Haka kuma an kai wadanda suka samu raunin babban asibitin Zinder domin yi musu magani.