Rashin lafiyar da jami'in Binance yake fama da ita a gidan yarin Nijeriya ta yi tsanani, in ji matarsa

Rashin lafiyar da jami'in Binance yake fama da ita a gidan yarin Nijeriya ta yi tsanani, in ji matarsa

"Ciwon bayan da ke damunsa ya yi taɓarɓarewar da wataƙila zai shafi yadda yake tafiya," a cewar Yuki Gambaryan.
Yuki Gambaryan ta yi  zargin cewa an hana lauyoyi su gana da mijinta tun ranar 26 ga watan Yuli./Hoto:EFCC/X

Rashin lafiyar da jami'in Binance Tigran Gambaryan yake fama da ita a gidan yarin Nijeriya inda ake tsare da shi bisa zargin cin-hanci ta yi tsanani, kamar yadda matarsa ta bayyana a ranar Litinin.

Hukumomi a Nijeriya suna tuhumar Binance da jami'ansa guda biyu - Gambaryan, ɗan ƙasar Amurka kuma jami'i kan kiyaye badaƙalar harkokin kuɗi na kamfanin, da Nadeem Anjarwalla, wani ɗan Birtaniya ɗan asalin Kenya wanda shi ne shugaban reshen Afirka na kamfanin da laifin halatta kuɗaɗen haramun da suka kai $35m.

A wata tuhuma ta daban, ana zargin Binance da zille wa biyan haraji a ƙasar.

Binance da Gambaryan sun musanta zarge-zargen. Anjarwalla ya tsere daga gidan yari kuma ya fita daga Nijeriya kafin a soma shari'arsu.

"Rashin lafiyar da yake fama da ita tana ƙara ta'azzara kuma kullum jikinsa na ci gaba da yin tsanani," in ji wata sanarwa da matar Gambaryan, Yuki Gambaryan, ta fitar.

"Ciwon bayan da ke damunsa ya yi taɓarɓarewar da wataƙila zai shafi yadda yake tafiya," a cewar Yuki Gambaryan.

Ta yi zargin cewa an hana lauyoyi su gana da mijinta tun ranar 26 ga watan Yuli.

Hukumar kula da gyaran hali ta Nijeriya ba ta mayar da martani game da wannan zargi ba kawo yanzu.

A watan Maris Binance ya ce zai daina duk wata hada-hada da kuɗin Nijeriya sakamakon matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na far wa masu harka da kirifto waɗanda ta zarga da hannu a tashin farashin dala a ƙasar lamarin da yake haddasa hauhawar farashin kayayyaki.

Alƙalin kotun, mai shari'a Emeka Nwite ya umarci a bayar da takarda mai ɗauke da bayanai game da kiwon lafiyar Gambaryan bayan ya gurfana a gaban kotun da ke Abuja a kan keken guragu daga gidan yarin Kuje. Sai dai ba a ba da takardar ba, kamar yadda kotun ta bayyana.

Alƙalin ya yi umarni a kai Gambaryan asibiti na tsawon awa 24 domin duba lafiyarsa.

Reuters