Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Traore tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin

Kasar Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a Burkina Faso a ranar Alhamis bayan shafe kusan shekaru 32, a cewar sanarwar gwamnatin kasar da ke yankin Afirka ta Yamma da kuma jami’in diflomasiyyar Rasha suka fitar.

An rufe ofishin ne a shekarar 1992, a cewar Jakadan Rasha a makwabciyar kasar Ivory Coast Alexei Saltykov, shugaban Rasha Vladimir Putin zai nada sabon jakadan Rasha a Burkina Faso.

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta fitar ta tabbatar da cewa "Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a yau Alhamis a Ouagadougou."

Saltykov ya ce zai jagoranci ayyukan diflomasiyyar Rasha a Burkina Faso har sai an nada sabon jakadan, yana mai bayyana Burkina Faso a matsayin "tsohuwar abokiyar hulda da muke da kyakkyawar alaƙa ta abota."

Sauya abokan hulda

A bara Burkina Faso ta fuskanci juyin mulkin soji har sau biyu -- sun samo asali ne sakamakon rashin gamsuwa da kuma gazawar da aka yi wajen kawo karshen matsalar tsaro ta masu tada ƙayar baya.

Tun bayan hawan su mulki a watan Satumban 2022, gwamnatin mulkin sojin kasar ta nesanta kanta daga Faransa, daɗaɗɗiyar abokiyar huldarta, sannan wacce ta mata mulkin mallaka, kana ta matsa kusa da Rasha.

A watan Oktoba ne Burkina Faso ta kulla yarjejeniya da kasar Rasha kan gina tashar makamashin nukiliya domin kara samar da makamashi a yankin Sahel inda kasa da kashi daya cikin hudu na al'ummar kasar ke samun wutar lantarki.

TRT Afrika