Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya ta tabbatar da cewa akalla farar hula 85 sojojin kasar suka kashe a wani hari bisa “kuskure” da sojojin suka ce sun kai a kasar a ranar Lahadi.
Rahotannin da aka samu daga farko sun ce mutum 30 aka tabbatar sun rasu a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin.
“Ofishin Arewa Maso Yammaci ya samu bayanai daga karamar hukuma kan cewa an binne gawarwaki 85 a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike”, kamar yadda NEMA ta bayyana a wata sanarwa a ranar Talata.
Hukumar ta ce akalla mutum 66 suke karbar magani a asibitoci da ke Kaduna.
Binciken hukumomi
Tuni shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru inda ya ce “abin takaici ne”.
A ranar Litinin, Kwamishinan wucin-gadi na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan yadda aka kashe wadannan farar hula.
Kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna VU Okoro ya tabbatar da cewa sojojin na gudanar da ayyuka ne a kan ‘yan ta’adda amma bisa kuskure suka kai hari kan farar hula.
Ziyarar shugaban sojojin kasa na Nijeriya
Shugaban sojojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya kai ziyara kauyen na Tudun Biri da safiyar Talata.
A lokacin ziyarar, ya hadu da Dangaladiman Zazzau hakimin Rigasa Architect Aminu Idris da sauran jama'ar kauyen.
Shugaban sojin ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda lamarin ya faru inda ya ce tuni sun soma gudanar da bincike kan lamarin.