Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da tsawaita dokar ta- bacin da ta sanya a wasu jihohin kasar da suke fama da matsalar hare-haren kungiyoyin masu tayar da kayar ba.
Ta bayyana haka ne bayan taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Alhamis wanda Shugaba Mohamed Bazoum ya jagoranta.
Jihohin da lamarin ya shafa su ne Diffa, Tawa da Tillaberi.
Dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa ranar 29 ga watan Yuli na 2023.
Gwamnati za ta mika bukatar tsawaita dokar ta-bacin ga majalisar dokoki don neman amincewar ta.
TRT Afrika