Sabbin masu bayar da shawara kan ayyukan soji da kayan aikinsu sun isa Nijar daga Rasha, kamar yadda tashar talabijin din kasar ta sanar, a lokacin da kasar ta nemi dakarun Amurka da su fice daga cikinta.
Rukunin farko na masu bayar da shawara su kimanin 100 sun isa Nijar a ranar 10 ga Afrilu tare da garkuwar makamai masu linzami.
A ranar Asabar jiragen soji na dakon kaya sun isa kasar, kamar yadda Tele Sahel ta sanar, inda ya zuwa yanzu Rasha ta aika da jiragen soji na daukar kaya uku da ma'aikata a wata dayan da ya gabata.
'The Africa Corps' da ake yi wa kallon wadanda suka maye gurbin mayakan Wagner a Afirka, sun tabbatar da zuwan masu bayar da horon a wani sako ta kafar Telegram.
Amurka ta janye dakarunta daga Nijar
A ranar Asabar, ta ce karin masu bayar da horo, da abnci sun isa kasar.
Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi nuni da cewa a ranar Alhamis dakarun Rasha sun samu gindin zama a sansanin sojin saman Nijar kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Yamai da ke dauke da sojojin Amurka.
Gwamnatin sojin Nijar da ta kwace mulki a watan Yulin 2023, ta kori dakarun Faransa daga kasar, sannan daga baya ta bayyana kawo karshen hadin gwiwar soji da Amurka. Ta ce wannan abu ne da Amurkan ta tilasta a yi shi.
A watan Afrilu Amurka ta amince ta kwashe sojojinta kimanin 1,000 daga Nijar.
Cibiyar jiragen yaki marasa matuka
Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Nijar game da janyewar.
Dakarun Amurka na da cibiyar jiragen sama marasa matuka a kusa da Agadas, wanda ta gina kan kudi kusan dala miliyan $100.
Shugabannin sojin Nijar sun kusanci Rasha, kamar yadda makotanta Mali da Burkina Faso suka yi, wadanda su ma suke karkashin mulkin sojoji, kuma dukkan su na yaki da 'yan tawaye.
A watan Afrilu, aka aika da Idrissa Soumana Maiga, shugaban jaridar gidan L'Enqueteur kurkuku bayan rubuta wata makala da ta ambaci batun saka na'urorin sauraren bayana na rasha a gine-ginen gwamnati.