Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun yi maraba da sanarwar da Faransa ta yi cewa za ta janye dakarunta daga kasar nan da karshen shekarar nan inda suka bayyana hakan da cewa "sabon mataki ne na samun kasa mai 'yanci".
Sun fitar da wannan sanarwa ce ranar Lahadi a gidan talabijin na kasar jim kadan bayan shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar cewar nan gaba kadan zai janye jakadansa daga Nijar, sannan ya kwashe dakarunsa daga kasar nan da watanni masu zuwa.
"A wannan Lahadin, muna murnar sabon mataki da zai kai ga samun kasa mai 'yanci," in ji sanarwar da sojojin suka fitar.
Ta kara da cewa "dakarun Faransa da jakadan kasar za su fita daga kasar Nijar nan da karshen shekara."
Sanarwar ta ce: "Wannan lokaci ne na tarihi, wanda ke nuna zage dantse da jajircewar al'ummar Nijar."
Tun da farko gabanin sanarwar da Macron ya fitar, hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama ta Afirka (ASECNA), ta sanar cewa sojojin Nijar sun haramta wa "jiragen Faransa" yin shawagi a sararin samaniyar kasar.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ne bayan sojojin sun kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.
Faransa ta yi Allah wadai da juyin mulkin sannan ta ce ba za ta yarda da wata gwamnati a Nijar ba idan ba ta Mohamed Bazoum ba ce.
Lamarin ya sa sojojin Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte ya fita daga kasar bayan da "ya ki amsa gayyatar" ma'aikatar harkokin waje don halartar wani taro da kuma "wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar".
Sai dai a wancan lokacin Shugaba Macron ya ce ba zai janye jakadan nasa daga kasar ba, yana mai jaddada cewa kasarsa tana kallonsu a matsayin haramtattu.
Dubban 'yan kasar Jamhuriyar Nijar sun kwashe makonni suna gudanar da zanga-zanga domin kira ga Faransa ta fita daga kasar.
Faransa tana da dakaru kusan 1,500 a Nijar wadanda suke yaki da kungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.
Ita ma kungiyar raya kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanya wa kasar takunkumai -- wadanda suka hada da rufe iyakokin wasu kasashen da ke kungiyar ga da Nijar sannan Nijeriya ta katse lantarkin da take bai wa kasar -- kuma ta sha alwashin yin amfani da karfin soji a kan kasar.
Sai dai sojojin, wadanda suka samu goyon baya daga Mali da Burkina Faso, sun sha alwashin mayar da martani mai karfi kuma cikin sauri.