Rikici tsakanin ƙasashen biyu ya samo asli ne tun watan Yulin 2023 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a Nijar, abin da ya sa ECOWAS ta sanya wa ƙasar takunkumai na fiye da watanni shida./Hoto:TRT Afrika

Nijar ta dakatar da fitar da fetur zuwa China ta batutan manta da suka ratsa ƙasar Benin, a cewar Ministan Albarkatun Fetur na ƙasar Mahamane Moustapha Barke Bako, lamarin da ake gani zai ta'azzara rikicin da ke tsakanin ƙasashen.

Ministan ya sanya kwaɗo ya rufe bututan man ƙasar da ke rijiyar mai ta yankin Agadem da ke gabashin ƙasar. Bututan man suna da nisan kilomita 2,000 waɗanda ta cikinsu ne Nijar take tura fetur China a wata yarjejeniya da ƙasar ta ƙulla da kamfanin mai na China National Petroleum Corp (CNPC) wadda ta kai $400m.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu a watan Mayu bayan hukumomi a Benin sun hana Nijar yin amfani da ƙasarsu domin fitar da fetur zuwa ƙasashen wajehar sai sojojin Nijar sun sake buɗe iyakarsu da Benin domin bari a shigar da kayayyaki tare da kyautata alaƙarsu.

A farkon watan Yuni, hukumomi a Benin sun tsare wasu 'yan ƙasar Nijar biyar bisa zargin yin leken asiri a wurin da bututan man fetur ɗinsu yake a iyakar Seme-Kpodji - ko da yake Nijar ta musanta zargin, inda ta ce mutanen masu sanya ido ne kan yadda ake lodin fetur kamar yadda suka yi yarjejeniya da Benin.

"Ba za mu zura ido muna kallon wasu mutane suna sace manmu ba, domin ba ma wurin da ake lodinsa," in ji ministan, a tattaunawa da ma'aikata, yayin da yake bayyana dalilansu na dakatar da fitar da fetur ɗin.

Rikici tsakanin ƙasashen biyu ya samo asli ne tun watan Yulin 2023 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a Nijar, abin da ya sa ECOWAS ta sanya wa ƙasar takunkumai na fiye da watanni shida.

Daga bisani ta ɗage takunkuman inda aka sanya ran cewa al'amura za su koma daidai, amma Nijar ta ƙi buɗe iyakarta da Benin.

TRT Afrika da abokan hulda