Bola Tinubu ya ce yana neman magance wani mawuyaci al'amari ne./Hoto:Fadar Shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce kasashen kungiyar ECOWAS sun shirya yin amfani da karfin soji kan sojojin da suka kifar da gwamnati a Nijar amma shi ne yake yi musu “linzami.”

Ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin da tawagar Malaman addinin Musulunci na Nijeriya da ya tura Nijar don ganawa da sojojin da suka yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki ta mika masa cikakken rahoto kan ziyarar da ta kai Yamai.

Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya shaida wa tawagar karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau cewa yana so a ci gaba da tattaunawa don samun mafita game da rikicin siyasar Nijar kafin ya lalubo wasu hanyoyin.

Labari mai alaka: Ko ECOWAS za ta iya dawo da Bazoum kan mulki?

"Ina neman magance babban al'amari ne. Idan ka cire batun ECOWAS, sauran mutane za su yi martani, wadanda ba a ce musu su bari. Ni ne nake yi wa wadannan bangarori linzami. Ni ne nake hana ECOWAS daukar mataki," a cewar Tinubu kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Ya kara da cewa: "Ko a safiyar yau, kasashen da sojojinsu suka shirya bayar da gudunmawa sun kira ni ta wayar tarho. Amma na gaya musu su dakata. Na ce musu zan gana da malamai sannan na kira su daga baya."

Shugaba Tinubu ya shaida wa tawagar malaman cewa dole ne sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su dauki alhakin jefa 'yan kasar Nijar cikin mawuyacin hali.

"Ba zai yiwu su yi amfani da bindigogin da aka ba su domin kare martabar kasa a kan 'yan kasar ba," in ji shi.

Ya umarci tawagar ta sake komawa Nijar don ci gaba da sulhu da sojojin yana mai cewa: "zan shata layi a cikin kasa sannan na umarce ku da ku sake shirin komawa Jamhuriyar Nijar."

Tawagar Malaman ta gaya wa Shugaba Tinubu cewa a shirye sojojin Nijar suke su tattauna da kungiyar ECOWAS a yayin da ake "daukar karin matakai na hana rikici da makami."

TRT Afrika