Shugaban Nijeriya wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Bola Tinubu, ya bayyana manyan nasarorin da ya samu tun da ya zama shugaban ƙungiyar shekara ɗaya da ta wuce.
Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a zauren taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) a Accra, babban birnin Ghana ranar Lahadi, in ji wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar.
Ya ce ƙungiyar ta kafa rundunar tsaro ta ko-ta-kwana domin yaƙi da ta'addanci kuma za su samo hanyoyi daban-daban na kuɗin gudanar da ita.
Shugaban na Nijeriya ya ce ECOWAS ta ƙarfafa gwiwar mambobinta domin inganta tsare-tarensu na gudanar da zaɓuka da mulki, yana mai cewa a kwanakin baya ƙungiyar ta tura wakilai domin sanya ido a kan zaɓukan da aka yi a Senegal da Togo - waɗanda aka yi amannar cewa sahihai ne.
Kazalika ya ce ƙungiyar ta shiga tsakani wajen sanya hannu kan yarjejeniyar Haɗin-kan Ƙasa a Sierra Leone, yana mai ƙarawa da cewa ECOWAS za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa-da-tsaki a ƙasar domin aiwatar da sharuɗɗan da ke cikin yarjejeniyar.
A fannin tattalin arziki, Shugaba Tinubu ya ce ECOWAS ta aiwatar da manufofi da dama da suka ƙarfafa cinikayya mara shinge tsakanin ƙasashe mambobinta, da inganta ayyukan ƙungiyar hukumomin kwastam na yankin da kasuwar gama-gari.
"Mun goyi bayan ƙasashe shida mambobinmu domin sanya hannu kan yarjejeniyar kamun kifi da Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO), sannan ƙasashe goma sha uku sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba ta Afirka (AFCFTA)," in ji Tinubu.
Da yake bayani kan agajin jinƙai da walwala, Shugaba Tinubu ya ce ECOWAS ta ware dala miliyan tara domin taimaka wa 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani.
Shugaban ECOWAS ya ce, "Kazalika an bayar da dala miliyan 4 ga ƙasashen da ke fama da hare-hare domin yaƙi da ta'addaci a ƙarƙashin shirin Yaƙi da Ta'addanci Da Bayar da Jinƙai na ECOWAS."
Shugaba Tinubu ya ce ECOWAS tana taimaka wa mabobinta wajen inganta ilimi da fasaha da makamashi da bai wa mata sana'o'i da sauransu.
Sai dai ya ƙara da cewa ƙungiyar tana ci gaba da fuskantar ƙalubale, ciki har da yadda wasu mabobinta suka fita daga cikin ƙungiyar, da hamayya tsakanin ƙasashe da ta'addanci, da rashun abinci da sauyin yanayi da watsuwar labaran ƙarya da sauransu.
Ya ce ECOWAS za ta ci gaba da tattaunawa da Burkina Faso, Mali, da Nijar domin tabbatar da haɗin-kai.