Rahotanni sun ce an yi garkuwa da Nabeeha da 'yan uwanta mata ne ranar 2 ga watan Janairu a gidansu da ke Abuja./Hoto: Asiya Adamu.X

'Yan Nijeriya sun soma matsa lamba ga rundunar 'yan sandan kasar bayan wasu rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutane sun kashe daya daga cikin 'yan mata shida da suka kama a kan hanyarsu ta komawa Abuja daga Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa an sace Nabeeha da mahaifinta da 'yan'uwanta ne ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.

Sai dai daga bisani sun saki mahafin nasu sannan suka bukaci a biya su naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa kafin su saki 'yan matan.

Tun daga lokacin ne wata makusanciyarsu mai suna Asiya Adamu ta kaddamar da kamfe a shafukan sada zumunta musamman shafin X, wanda a baya ake kira Twitter, tana neman mutane su taimaka su hada kudin domin kai wa 'yan bindigar, wadanda suka yi barazanar kashe su.

Sai dai ranar Asabar Asiya ta wallafa sako da ke cewa 'yan bindigar sun kashe Nabeeha.

Shi ma Farfesa Isa Ali Pantami, tsohon minista a Nijeriya, ya tabbatar da kisan Najeebah a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

"Yanzu na karanta labarin kisan 'yarmu Nabeeha (daliba 'yar aji 400 a ABU). Na yi magana da mahaifinta game da sauran 'ya'yanmu biyar da aka yi garkuwa da su. Allah ya gafarta mata, ya kubutar da sauran 'yan matan sannan ya kawo zaman lafiya a Nijeriya," in ji Pantami.

Neman dauki

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin 'yan kasar inda suka rika yin kiraye-kiraye ga rundunar 'yan sandan kasar ta kubutar da sauran 'yan matan da ke hannun masu garkuwa da mutane.

Malam Bashir Ahmad, mai taimaka wa tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kan shafukan sada zumunta, na daya daga cikin wadanda suka ja hankalin rundunar 'yan sandan kasar game da wannan batu.

Ya wallafa sako a shafinsa na X inda ya roki rundunar ta yi gaggawar tsoma baki a lamarin tare da kubutar da sauran 'yan matan bayan "masu garkuwa da mutane sun kashe Najeebah a matsayin gargadi sannan suka bukaci a biya N100m a matsayin kudin fansa na sauran wadanda aka yi garkuwa da su".

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ya ce suna bibiyar batun satar 'yan matan amma "muna bukatar wasu bayanai. Ya kamata 'yan'uwan (matan da aka sace) su yi magana da ni kai-tsaye, su tura mini sako."

Adejobi ya ce "za mu yi bakin kokarinmu don daukar matakan da suka dace wajen ganin an kubutar da su ba tare da ko kwarzane ba."

TRT Afrika