Akalla mutane 48 ne suka mutu sakamakon ruftawar ƙasar a wani wurin da ake haƙar zinari ba bisa ƙa’ida ba a yammacin kasar Mali a ranar Asabar, kamar yadda hukumomi da majiyoyi na cikin gida suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kasar Mali dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da zinari a nahiyar Afirka, kuma ana yawan samun zaftarewar ƙasa a wuraren haƙar zinaren, inda mutane da dama ke rasa rayukansu.
Hukumomin kasar sun yi ta ƙoƙarin daƙile haƙo karafa masu daraja a kasar ba tare da bin ka'ida ba a ƙasar da ke cikin ƙasashen duniya mafi fama da talauci.
“Yau da misalin 6:00 na safe mutum 48 aka tabbatar sun rasu bayan ruftawar,” kamar yadda wata majiya ta ‘yan sanda ta bayyana.
"Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun fada cikin ruwa, daga cikinsu akwai wata mata dauke da jaririnta a bayanta."
Wani jami’in yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da kungiyar masu haƙar gwal ta Kenieba ita ma ta ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 48.
Ana ci gaba da neman wadanda abin ya shafa, kamar yadda shugaban wata kungiyar kare muhalli ya shaida wa AFP.
Hatsarin na ranar Asabar ya faru ne a wani wurin haƙar ma’adinai da aka daina amfani da shi wanda wani kamfani na kasar Sin ya ci moriyarsa a baya, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.
A watan Janairu, wata zaftarewar kasa a wata mahakar zinari da ke kudancin kasar Mali ta kashe mutane aƙalla mutum 10 tare da ɓacewar wasu da dama, mafi yawansu mata.