Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane da dama sun kulle masu aiki 'yan ci-ranin Afirka a gidajensu a Lebanon yayin da masu gidan ke tserewa daga hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.
Hukumar Kula da Ƙaura ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana ƙara nuna halin ko-in-kula ga ma'aikatan cikin gida na ƙasashen waje don fuskantar haɗari a cikin rikicin.
Hukumar ta IOM ta yi tsokaci kan halin da ma'aikatan bakin haure 170,000 na kasar Lebanon ke ciki, wadanda yawancinsu mata ne daga kasashe irinsu Habasha, Kenya, Sri Lanka, Sudan, Bangladesh da Philippines.
Mathieu Luciano, shugaban ofishin IOM a Lebanon ya ce "Muna samun karuwar rahotannin ma'aikatan gida na bakin haure da ma'aikatansu 'yan kasar Lebanon suka yi watsi da su, ko dai a bar su a kan tituna ko kuma a cikin gidajensu yayin da iyayen gidan nasu ke gudu."
'Yan ci rani na neman taimako
"Suna fuskantar karancin matsuguni," kamar yadda ya shaida wa wani taron manema labarai a Geneva, ta bidiyo daga Beirut, ya kara da cewa a ranar Alhamis ya ziyarci wani matsuguni a babban birnin kasar da ke dauke da iyalai 'yan Sudan 64 "wadanda ba su da wurin zuwa".
Ya ce hukumar ta IOM na samun karuwar bukatu daga bakin haure da ke neman taimako na komawa gida. Kasashe da dama kuma sun nemi taimakon hukumar domin kwashe ‘yan kasar.
Duk da haka, "wannan yana buƙatar kudade masu yawa - wanda a halin yanzu ba mu da su," in ji shi.
Kusan shekara guda bayan da Hamas ta kai wa Isra’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, Isra’ila ta sanar da cewa ta karkata akalarta wajen tabbatar da tsaron iyakarta da Lebanon.
Dubban mutane sun gudu daga gidajensu
Hare-haren da Isra'ila ta kai kan maboyar Hezbollah a kasar Lebanon ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 1,000 tun daga ranar 23 ga watan Satumba, a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon, yayin da dubban mutane suka tsere daga gidajensu a kasar da tuni ta fada cikin matsalar tattalin arziki.
Halin da ma'aikatan 'yan ci-rani na kasar Lebanon ke ciki mai muni ne, domin a lokuta da dama ana danganta matsayinsu na shari'a da iyayen gidansu.
“Mun ga a kudu yadda mutane ke guduwa amma ko dai su bar masu aikinsu a kan tituna, ba sa tafiya tare da su – ko kuma abin da ya fi muni, su kulle masu aikin a cikin gida, don su kula musu da gidajen nasu yayin da suke neman mafaka a wani wuri daban," in ji shi.
Ma'aikata marasa izini
Luciano ya ce wadanda aka bari a kan titi za su yi gwagwarmayar ƙaura ko kuma su kai ga tsira, yayin da da yawa ba sa jin Larabci.
"Da yawa ba su da takardun shaida, ba su da takarda. Sakamakon haka ba su da sha'awar neman agaji saboda suna fargabar za a kama su kuma za a iya fitar da su," in ji shi.
Luciano ya lura cewa akwai "manyan batutuwa game da lafiyar kwakwalwa" a tsakanin masu aikin gida baƙin haure da ke aiki a Lebanon.