A ranar 26 ga watan Yuli ne duniya ta wayi gari da labarin cewa wasu sojoji da ke tsaron fadar shugaban Nijar sun toshe duk wasu hanyoyi na shiga da fita daga cikinta.
Daga bisani bayanai suka tabbatar da cewa juyin mulki shugaban sojojin da ke kula da fadar shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya jagoranci yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.
Juyin mulkin ya ja hankalin duniya sosai kuma har yanzu ana neman hanyar warware rikicin siyasar da kasar ta fada a ciki.
Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kama manyan jami'an gwamnatin Bazoum
Mun yi nazari kan wasu muhimman abubuwa da suka faru tun daga lokacin da aka kifar da gwamnatin dimokuradiyya a Nijar:
- 26 ga Yuli – An hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga kan mulki
- 28 ga Yuli – Tiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Nijar
- 30 ga Yuli – ECOWAS ta bai wa sojoji wa’adin mako guda su mika mulki ko ta yi amfani da karfin soji akansu - bayan ta sa wa kasar takunkumai
- 31 ga Yuli – Mali da Burkina Faso sun yi gargadi kan amfani da karfin soji a kan Nijar - inda suka ce kai wa Nijar hari tamkar ayyana yaki a kansu ne
- 31 ga Yuli– An ga Bazoum a karon farko tun bayan kifar da gwamnatinsa inda ya gana da shugaban Chadi Mahamat Deby
- 1 ga Agusta – Faransa da wasu kasashen Yamma sun soma kwashe ‘ya’yansu daga Nijar
- 3 ga Agusta – An hana tawagar ECOWAS karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar ganin Bazoum da Tiani
- 8 ga Agusta – An nada Mohamed Lamine Zein a matsayin Firaiministan Nijar
- 12 ga Agusta – Sojoji sun ce a shirye suke su tattauna da ECOWAS bayan Malaman addinin Musulunci na Nijeriya sun kai musu ziyara
- 19 ga Agusta – Janar Tiani ya yi alkawarin mika mulki cikin shekara uku bayan ya gana da tawagar ECOWAS
- 22 ga Agusta – Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Nijar daga cikinta
- 25 ga Agusta – Sojojin Nijar sun bai wa jakadan Faransa wa'adin awa 48 ya fita daga kasar
TRT Afrika