Abubuwa da dama ciki har da zanga-zanga daban-daban duk sun faru tun bayan hambarar da gwamnatin al bashir a 2019. Photo/AP

Ana ci gaba da rikici a babban birnin Sudan, watanni 18 bayan juyin mulkin soji, wanda hakan kuma ya kara nisanta kasar da zabe na dimokradiyya da kuma kara rura wutar rikici a kasar da ke Gabashin Afirka.

Shugabanni daga bangaren sojojin Sudan da kuma rundunar Rapid Support Forces wato RSF suna zaman doya da manja kan batun hade rundunonin biyu su zama tsintsiya madaurinki daya.

Sojojin da RSF ne suka hada kai wurin hambarar da gwamnatin farar hula ta Omar al Bashir a 2019 bayan zanga-zanga da aka gudanar a kasar.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 2021:

25 ga Oktoba, 2021: Juyin Mulki

A ranar 25 ga watan Oktoban 2021, an gudanar da juyin mulki na biyu wanda Janar Abdel Fattah al Burhan, shugaban majalisar soji ya jagoranta.

Sojojin sun sauke kwamitin hadaka na soji da farar hula da ke gudanar da mulkin kasar inda suka kama jagororin ciki har da Firaiminista Abdalla Hamdok.

Daga nan aka saka dokar ta-ba-ci inda daga nan kuma zanga-zanga ta biyo bayan juyin mulkin da aka yi sa’annan kasashe da kungiyoyi masu zaman kansu suka biyo da Allah-wadai.

Jami’an tsaro sun kashe masu zanga-zanga bakwai da kuma raunata gwammai a rikicin. Amurka da Bankin Duniya duk sun dakatar da tallafi ga Sudan.

11 ga Nuwamba: Sabuwar majalisar mulkin soji

Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Sudan. Majalisar Dinkin Duniya da kuma Amurka duk sun yi kira ga sojojin da ke mulki a Sudan da su mayar da mulki a hannun farar hula.

A ranar 11 ga watan Nuwamba, jagoran kasar al Burhan ya kaddamar da sabuwar majalisar mulkin soji. Burhan ne ke jagorantar majalisar.

Sai dai bangaren da ke hankoron mayar da mulki a hannun farar hula ba a saka shi a cikin majalisar ba.

21 ga Nuwamba: Firai minista ya dawo

A ranar 21 ga watan Nuwamba, Burhan ya amince da a mika mulki ga farar hula, inda aka saka zaben kasar Yulin 2023.

An dawo da Hamdok a matsayin firai minista. An saki jagororin farar hula da dama. An ci gaba da zanga-zanga kuma ana dakile su da karfi.

2 ga Janairu, 2022: Firai minista ya yi murabus

A daidai lokacin da adadin wadanda suke mutuwa sakamakon zanga-zanga ke karuwa, Hamdok ya yi murabus a ranar 2 ga watan Janairun 2022.

Tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wadda manyan kungiyoyin farar hula suka kauracema, ta fara a farkon watan Yuni, amma ba ta yi karko ba.

4 ga Yuli: Sojoji su koma gefe

A ranar 4 ga watan Yuli, Burhan ya bayyana cewa sojoji za su daina tattaunawa domin barin kungiyoyin farar hula su kafa gwamnati.

Babbar kungiyar ta farar hula ta ce tana zargin akwai wata makarkashiya a kasa. Bankin Duniya ya ware dala miliyan 100 domin tallafi ga Sudan.

5 ga watan Disamba: Yarjejeniyar wucin gadi

Sojojin Sudan da sauran jami’ai masu damara da kuma akasarin jagororin farar hula sun saka hannu kan wata yarjejeniya ta wucin gadi a ranar 5 ga watan Disamba wadda ke da burin mayar da mulki ga farar hula cikin shekara biyu.

Masu zanga-zanga sun hau kan tituna, inda suke korafi kan cewa yarjejeniyar ba ta tabo batun yin adalci ga mutum 120 da aka kashe masu goyon bayan dimokradiyya ba tun bayan juyin mulkin Hamdok.

Janairun 2023: Tattaunawa

Shugabannin soji da na farar hula a farkon watan Janairun 2023 sun hadu domin tattaunawa kan wasu muhimman abubuwa da suka hada da adalci, yin komai a kididdige da kuma sauyi ga fasalin tsaro, ciki har da mayar da rundunar RSF da ake shakka cikin sojoji.

13 ga watan Afrilu: Zaman dar-dar mai hastari

An shiga cikin fargaba tsakanin sojoji da kuma RSF kan batun mayar da su wuri guda.

Mataimakin Burhan, Mohamed Hamdan Daglo wanda shi ne kwamandan RSF ya bayyana cewa juyin mulkin da aka yi a 2021 “kuskure” ne da ya kara karfafa sauran burbushin mulkin Bashir, kalaman da ake kallo kan cewa da Burhan yake.

Sau biyu ana dage batun saka hannu kan mika mulki ga farar hula.

15 ga watan Afrilu: Rikici a Khartoum

A ranar 15 ga watan Afrilu, an soma jin karar fashewa da harbin bindiga a Khartoum babban birnin Sudan, inda RSF da sojojin kasar suka yi ta musayar yawu kan kai wa juna hari.

RSF din ta bayyana cewa ita ke da iko da filin jirgin Khartoum da kuma fadar shugaban kasa, ikirarin da sojojin kasar suka musanta. Haka kuma sojojin saman Sudan sun kai hare-hare sansanonin RSF.

Shugabannin farar hula da Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya duk sun yi kira kan a tsagaita wuta nan take.

TRT World
TRT Afrika da abokan hulda