Mpox: Cutar farankamar biri na ƙaruwa a Nijeriya, in ji NCDC

Mpox: Cutar farankamar biri na ƙaruwa a Nijeriya, in ji NCDC

Amma duk da ƙaruwar cutar ta farankamar biri, kawo yanzu ba a samu wanda ya mutu ba.
Mpox / Photo: Reuters

Hukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce an samu ƙaruwar mutanen da suka kamu da cutar farankamar biri wato mpox a jihohi 20 da kuma Babban Birnin Tarayya, inda yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 48.

NCDC ta bayyana haka ne a saƙon da ta fitar a shafukanta na sada zumunta ranar Juma'a.

Amma duk da ƙaruwar cutar ta farankamar biri, kawo yanzu ba a samu wanda ya mutu ba.

Hukumar ta ce a mako ɗaya daga ranar 19 zuwa 25 ga watan Agusta kaɗai mutum takwas ne suka kamu da cutar, inda aka samu masu cutar guda huɗu a jihar Enugu, sai ɗai-ɗai a jihohin Bayelsa, Cross River, Edo da Osun.

Ta ƙara da cewa cutar ta fi shafar yara daga shekara ɗaya zuwa shekara biyar.

NCDC ta bayar da sanarwar ce a yayin da ƙasar ta karɓi allurai 10,000 na rigakafin farankamar biri daga Amurka ranar 27 ga watan Agusta.

Tuni dai Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ayyana cutar a matsayin wani lamari da ke buƙatar ɗaukin gaggawa a yayin da take ci gaba da yaɗuwa a sassan Afirka.

Mece ce mpox?

Mpox cuta ce da ake ɗauka daga ƙwayar cutar bairos. Kuma alamunta su ne zazzaɓi, da ciwon kai da ciwon baya da ciwon gaɓoɓi da kasala da yawan gajiya da kumburi.

Ƙuraje za su iya fesowa su kuma watsu a gaba ɗayan jiki, sai dai suna fin yawa a fuska, sannan daga baya su bushe su riƙa ɓarewa daga jiki.

Ƙwayar cutar mpox na janyo rashin lafiya a mafi yawan lokuta. Alamunta za su iya bayyana tsakanin kwana biyar zuwa 21 bayan kamuwa.

Ya take yaɗuwa?

Ƙwayar cutar za ta iya yaɗuwa idan mutum ya taɓa mai ɗauke da cutar ko ya taɓa wani abin da mai cutar ya taɓa ya kuma gurɓata shi.

Sai dai haɗarin yaɗa cutar ga jama’a ba shi da yawa. Ƙwayar cutar ta fi kama yara kuma zuwa kaso goma cikin ɗari na waɗanda suka kamu da mpox za su iya mutuwa.

A ina ake samun mpox?

Cutar Mpox ta samo asali ne daga dazuzzuka a ƙasashe masu zafi a Tsakiya da Yammacin Afirka kuma tana yaɗuwa tsakanin dabbobin daji.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu ba a gano ‘ainihin inda mpox take tasowa ba’ sai dai ƙwayar cutar ta fi yaɗuwa ne a tsakanin ɓeraye da birrai.

A ina aka fara gano mpox?

An fara gano cutar a 1958 bayan cuta mai kama da ƙyanda ta ɓarke a cikin birai da aka yi amfani da su wajen bincike.

An fara gano cutar a jikin mutane a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a 1970A ranar 13 ga Agusta, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta bayyana cutar a matsayin annoba a duka faɗin nahiyar.

A lokacin da ƙwayar cutar ta mpox nau’in clab 1b mai haɗari da saurin yaɗuwa a baya ta yaɗu daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo zuwa iyakokin ƙasashe maƙota kamar Burundi da Kenya da Rwanda Uganda.

Shin akwai maganin cutar?

A yanzu dai babu wani takamaiman maganin mpox. Akwai riga-kafi uku da ake da su da kuma a Janairun 2022 Hukumar Magunguna ta Turai ta amince a yi amfani da wani magani da aka samar na cutar agana don jinyar mpox, sai dai bai wadata ba a cikin jama’a.

Hukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce akwai matakan da za a iya ɗauka a matsayin riga-kafin cutar, waɗanda suka haɗa da:

  • Nisantar duk dabbodin da ke iya yaɗa cutar da suka haɗa da marasa lafiya da mushe a wuraren da aka samu mpox
  • Da nisantar duk wani abu da dabbar da ba ta da lafiya ta taɓa
  • Killace dabbobin da aka ga alamun sun kamu da cutar, kada su haɗu da sauran dabbobi.
  • Dafa naman dabbobi da ƙwansu da nononsu sosai kafin a ci ko a sha
  • Keɓe mutanen da suka kamu, da kuma saka kayan kariya duk lokacin da za a je wajensu
  • Wanke hannu a-kai-a-kai bayan kula ko ziyartar marasa lafiya
  • Wayar da kan mutane kan cutar da matakan kariya.
TRT Afrika