Jamhuriyar Kongo ce ƙasar da ke da adadi mafi yawa na masu farankamar biri a daidai lokacin da cutar ke ƙara yaɗuwa. / Hoto: AFP

Kusan mutane 30,000 da ake zargin sun kamu da mpox ne aka samu rahoton bullar cutar a Afirka ya zuwa yanzu a wannan shekarar, akasarinsu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya a ranar Litinin.

Sama da mutum 800 ne suka mutu sakamakon zargin kamuwa da mpox a fadin nahiyar a wancan lokacin, in ji hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a cikin rahotonta.

Ya ƙara da cewa maƙwabciyar ƙasar Congo da ke tsakiyar Afirka ita ma Burundi ta fuskanci ɓarkewar annobar.

Yawanci tana haifar da alamu masu kama da mura da ƙuraje masu kumbura jiki.

Mpox na iya yaduwa ta hanyar kusanci. Duk da cewa ba ta da tsanani, amma takan zama sanadin mutuwa a wasu lokutan.

Sanarwar ta WHO ba ta bayar da kwatancen alkaluma na shekarun baya ba. Hukumar kula da lafiyar jama'a ta Tarayyar Afirka ta ce an samu rahoton bullar cutar 14,957 da kuma mutuwar mutane 739 daga kasashe bakwai da cutar ta shafa a shekarar 2023 - adadin da ya karu da kashi 78.5 cikin 100 daga cikin 2022.

Kashe kudade don yaƙi da mpox

An samu mutane 29,342 da ake zargin sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 812 a fadin Afirka daga watan Janairu zuwa 15 ga watan Satumba na wannan shekara, a cewar rahoton na WHO.

Kimanin mutane 2,082 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin duniya a cikin watan Agusta kadai, mafi girma tun watan Nuwamba 2022, in ji WHO.

A ranar Asabar, asusun Bankin Duniya na annobar cutar ya ce zai bai wa kasashen Afirka goma dala miliyan 128.89 don taimakawa wajen yakar annobar.

TRT Afrika